Gwamnati ta baiwa shugaban NHIS hutu don yin bincike

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutum bakwai daga cikin masu fada aji na Hukumar Insorar Lafiya (NHIS), don yin binciken zargin da ake yi wa Shugaban (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. Mambobin kwamitin sun hada da: tsohon sakataren ma’aikatar Noma Dakta Bukar Hassan da Dakta Emmanuel Meribole da Mista Adewale Owolo da Mista Shamsuddeen Bello […]

Gwamnati ta baiwa shugaban NHIS hutu don yin bincike

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutum bakwai daga cikin masu fada aji na Hukumar Insorar Lafiya (NHIS), don yin binciken zargin da ake yi wa Shugaban (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.

Mambobin kwamitin sun hada da: tsohon sakataren ma’aikatar Noma Dakta Bukar Hassan da Dakta Emmanuel Meribole da Mista Adewale Owolo da Mista Shamsuddeen Bello da Mista Ishaq Yahaya, da Dakta Ekanem John Udoh, da kuma Misis Jummai Idakwo.

Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Mista Boss Gida Mustapha ya ce, a ranar Juma’a da karfe 3 na rana za a kaddamar da kwamitin a ofishinsa.