Gwamnati ta bayyana dalilin da ya sa Buhari ya soke tafiya Ruwanda
Shugaba Muhammadu Buhari ya soke tafiya zuwa kasar Ruwanda don halartar taron shugabannin kasashen Afirka inda zai sanya hannu kan kasuwancin zamani na baidaya don bayar da isashshen lokaci ga masu ruwa da tsaki a Najeriya. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Tope Adeleye Elias ya bayyana cewa a cikin wata sanarawar da […]

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke tafiya zuwa kasar Ruwanda don halartar taron shugabannin kasashen Afirka inda zai sanya hannu kan kasuwancin zamani na baidaya don bayar da isashshen lokaci ga masu ruwa da tsaki a Najeriya.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Tope Adeleye Elias ya bayyana cewa a cikin wata sanarawar da ya fitar a ranar Lahadi.
Ofishin yada labarai na fadar shugaban kasa ya bayyana a wata sanarwar da ya raba wa manema labarai da ke fadar.
An shirya Buharin zai tafi birnin Kigali a ranar Litini don halartar taron kungiyar shugabannin kasashen Afirka wanda za a gudanar ranar Talata mai zuwa don sanya hannu kan yarjejniyar kasuwancin zamani.