Gwamnati ta binciki yadda ake daukar jami’an tsaro aiki – Limamin JIBWIS Kuros Riba
An bukaci gwamnati tun daga matakin Shugaban Kasa da Gwamnonin jihohi su mayar da hankali wajen inganta wutar lantarki da tsaro a kasar nan kana a samarwa da matasa ayyukan yi domin magance matsalolin da ake fama dasu a kasar nan. Sheikh Bashir Salihu Abuga shugaban majalisar malamai ta Kungiyar Izala da ke Jihar Kuros […]
An bukaci gwamnati tun daga matakin Shugaban Kasa da Gwamnonin jihohi su mayar da hankali wajen inganta wutar lantarki da tsaro a kasar nan kana a samarwa da matasa ayyukan yi domin magance matsalolin da ake fama dasu a kasar nan. Sheikh Bashir Salihu Abuga shugaban majalisar malamai ta Kungiyar Izala da ke Jihar Kuros Riba ne ya bukaci hakan a tattaunawar su da wakilin Aminiya, jim kadan da kamala rufe tafsirin azumin watan Ramadan da aka yi ranar Juma’ar makon da ya gabata a harabar masallacin kungiyar.
Babban Limanin ya ci gaba da cewa, “Gwamnati ta inganta wutar lantarki a kasar nan kusan yanzu yadda ake samun wutar lantarkin lokutan basu da yawa gashi har makwabtan mu Jamhuriyar Nijar kasar nan ke ba wutar lantarki, amma mu gashi taki wadata a kasa.”
Malamin, ya ci gaba da jawo hankalin gwamnati da cewa, ta fuskar jami’an tsaro gwamnati ta sanya ido sosai wajen yadda ake daukar aikin su domin, yawanci ana samu’ yan Najeriya suna shiga aikin maimakon kare lafiya da tsare dukiyar jama’a sai a iske sun fi aikata barna yawanci ana samun baragurbi a cikin su domin haka wajibi ne gwamnati ta sanya ido wajen yadda ake daukar aikin tsaro,” in ji shi.
Sheikh Salihu Abuga, ya kara da cewa, “Matasa kuma a samar masu da aikin yi mafi yawan matasan kasar nan birjik sun gama manyan makarantu da jami’o’i amma basu da aikin yi kamata ya yi gwamnati ta samar wa matasan kasar nan guraben ayyukan yi hakan zai kawo karshen zargin shaye-shaye da ta’addanci da ake zargin matasan na yi.”
Ya yi fatan gwamnati a wannan wa’adin na mataki na gaba zata inganta tsaro ta magance garkuwa mutane ana yin garkuwa da su domin neman kudin fansa da yanzu al’amarin ya zama babban kalubale musamman a jihohin Arewa maso Yamma na kasar nan.