Gwamnati ta bude manyan makarantun da ke Kudancin Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya ba da umarnin a bude manyan makarantun jihar da aka rufe a Kudancin Kaduna sakamakon tashe-tashen hankulan da suka rika faruwa a yankin a watannin baya. Gwamna El-Rufa’i ya bayar da umarnin ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da ya karbi bakuncin wadansu dattawa daga […]

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya ba da umarnin a bude manyan makarantun jihar da aka rufe a Kudancin Kaduna sakamakon tashe-tashen hankulan da suka rika faruwa a yankin a watannin baya.
Gwamna El-Rufa’i ya bayar da umarnin ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da ya karbi bakuncin wadansu dattawa daga Kudancin jihar a gidan gwamnati.
Gwamnan ya ce babu shakka gwamnatinsa ta gamsu da dorewar zaman lafiya a yankin Kudancin jihar wanda ya yi fama da rikice-rikice a watannin baya.
Gwamnan ya kuma bayyana wa bakin nasa cewa babu wata al’umma da za ta ci gaba cikin tashin hankali musamman rikicin addini da kabilanci. “Wannan mataki an dauke shi ne bayan an gamsu da samun zaman lafiya a yankin, saboda haka muke godiya da shawarwarin da dattawa irinku suke bayarwa a yankin wadanda suke taimaka wajen maido da zaman lafiya a yankin. Ba za mu yarda wadansu su rika amfani da kabilanci da bambancin addini wajen cimma burinsu na son rai ba. Za mu tabbatar da hakan bai faru ba, saboda haka muna godiya kan irin goyon baya da muke samu daga wajenku domin samun tabbataccen zaman lafiya. Kuma za mu tabbatar da cewa dukan manyan makarantun gwamnatin jihar sun samu rassa a dukan kananan hukumomin jihar 23. Wannan mataki da muka dauka ya samu amincewar Majalisar Zartaswa ta Jihar kuma zai taimaka matuka wajen bai wa jama’a damar samun ilimi cikin sauki,” inji shi.
Gwamnan ya kuma ce kowane reshe na manyan makarantun za a hada shi da karamar hukuma daya a jihar domin ci gaba da kulawa, ya ce haka makarantu a kasashen Amurka da Birtaniya suke aiwatar da al’amuransu.
A cikin ayarin dattawan da suka ziyarci Gwamnan, akwai Kwamandan Sojan Sama (mai murabus), Emmanuel Jekada da Bishop din Cocin Katolika da ke Zaria, Bishop George Dodo da Mai shari’a Haruna Makers da Misis Grace Ambi da kuma Dokta Bege Katuka.
A watannin baya ne gwamnatin jihar ta rufe manyan makarantun ciki har da Kwalijin Ilimi da ke Gidan Waya da rashen Jami’ar Jihar da ke Kafanchan sakamakon tashe-tashen hankulan da suke faruwa a yankin.