Gwamnati ta caccaki shugabanni kan coronavirus

Gwamnatin Tarayya ta fusata kan yadda wasu shugabanni ke saba dokar kariyar cutar coronavirus na tantance mutane a filayen jiragen sama. Shugaban kwamitin yaki da cutar corornavirus da Shugaban Kasa ya kafa, Boss Mustapha ya bayya haka bayan Gwamnan Jiharsa ta Adamawa Ahmadu Fitiri da tsohon gwamnan Zamfara Abdulazeez Yari da wasu manyan mutane sun […]

Gwamnati ta caccaki shugabanni kan coronavirus

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Gwamnatin Tarayya ta fusata kan yadda wasu shugabanni ke saba dokar kariyar cutar coronavirus na tantance mutane a filayen jiragen sama.

Shugaban kwamitin yaki da cutar corornavirus da Shugaban Kasa ya kafa, Boss Mustapha ya bayya haka bayan Gwamnan Jiharsa ta Adamawa Ahmadu Fitiri da tsohon gwamnan Zamfara Abdulazeez Yari da wasu manyan mutane sun bijire wa matakan a filayen jiragen sama na Fatakwal da kuma Kano bayan dawo da zirga-zirgar jirage.

“Ya kamata shugabanni su zama kyawawan ababen koyi. Matukar muna so mu yaki wannan annoba to dole ne a matsayinmu na shugabanni da mabiya mu sauya dabi’unmu. Babu ruwan kwayar cutar da matsayi ko dangantaka illa kawai a kiyaye”, inji shi.

Boss Mustapha wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya ya tuna da cewa tun kafin a sake bude filayen jiragen sama sai da aka yi tsarin kiyaye kamuwa da cutar aka yi gwaje-gwaje domin tabbatarwa tare da kira ga manyan mutane da su mutunta dokokin.

A cikin wata sanarwa da ke martani ga dabi’un manyan mutane da ke karya matakan kariyar cutar, Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), ta ce ba za ta lamunta ba.

Shi ma a martasinsa, Shugaban Kwamitim Majalisar Wakilai kan Sufurin Jiragen Sama Nnolim Nnaji  ya bukaci da a hana duk wani shugaban da saba dokar wucewa a filayen jirgin.

Nnaji ya ce majalisar na goyon bayan ma’akiatan FAAN da na Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) wajen tabbatar da dokokin.

“Na tabbata Gwamnatin Tarayya ma tana goyon bayansu domin su ne a sahun gaba wajen yaki da cutar wanda gwamnati ta kase kudade domin tabbatar da matakan kafin bude tashoshin jiragen sama, saboda haka wajibi ne kowa ya kiyaye”.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos