Gwamnati ta dakatar da jarabawar WAEC
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da bude makarantu da kuma gudanar da jarabawar kammala sakandare ta WAEC. Ministan Ilimi Adamu Adamu bayan taron Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Kasa ya ce makarantun Gwamnatin Tarayya za su ci gaba da zama a rufe sai an samu tabbacin amincin dalibai daga cutar coronavirus. Bayan kwana 102 jirgin farko […]
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da bude makarantu da kuma gudanar da jarabawar kammala sakandare ta WAEC.
Ministan Ilimi Adamu Adamu bayan taron Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Kasa ya ce makarantun Gwamnatin Tarayya za su ci gaba da zama a rufe sai an samu tabbacin amincin dalibai daga cutar coronavirus.
A baya an sanar da fara jarabawar WAEC daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba.
Amma ministan ya ce hukumar shirya rabawa ta kasashen Yammacin Afirka (WAEC) ba ta da ikon yanke wa Najeriya hukuncin ranar bude makarantu.
Adamu Adamu ya kuma shawarci gwamnatocin jihohi da su jingine shirinsu na bude makarantu.
A bayan Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha mai jagorantar kwamitin shugaban kasa na yakar cutar COVID-19 ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bude makarantu ga dalibai masu rubuta jarabawar kammala karatun firamare da na sakandare.
Sai dai ya cewa nan gaba za a sanar da matakan da za a bi wajen bude makarantun.