Gwamnati ta dauki nauyin rainon yara ukun da mahaifiyarsu ta rasu a Malumfashi
Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki alkawarin ci gaba da kulawa da dawainiyar yaran nan ’yan hudu da aka haifa a garin Malumfashi makonni biyu da suka gabata, sakamakon rasuwar da mahaifiyarsu ta yi tare da daya daga cikin jariran a Lahadin da ta gabata. Alkawarin ya fito ne daga bakin Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya […]

Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki alkawarin ci gaba da kulawa da dawainiyar yaran nan ’yan hudu da aka haifa a garin Malumfashi makonni biyu da suka gabata, sakamakon rasuwar da mahaifiyarsu ta yi tare da daya daga cikin jariran a Lahadin da ta gabata.
Alkawarin ya fito ne daga bakin Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari, a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da ta je Malumfashi, domin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar yaran da kuma daya daga cikin jariran da suka rasa rayukansu, suka bar saura jariran uku.
Uwargidan ta mika ta’aziyyar Gwamna Aminu Bello Masari ga mijin marigayiyar, sannan ta gabatar masu da gudunmuwar kayayyakin amfanin yau da kullum tare da kudi cikin ambulan, wadanda ba ta bayyana adadinsu ba.
A lokacin da take karkare ziyarar ta’aziyyar, Hajiya Hadiza ta ce Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da daukar nauyin jariran uku har zuwa lokacin da za su yi wayau.