Gwamnati ta fitar ka’idoji shida na bude makarantu

Gwamnatin Tarayya ta gindaya sharudda shidda da cika su ya waja a  kan makarantu a dukkan matakai kafin a sake bude su. A ranar 19 ga watan Maris, 2020 ne gwamnatin ta rufe dukkan makarantu a kokarinta na dakile yaduwar cutar coronavirus. Karamin Ministan Lafiya Chukwuemeka Nwajiuba ya ce kafin a sake bude makarantu dole […]

Gwamnati ta fitar ka’idoji shida na bude makarantu

Wasu daliban makarantar firamare.(Tsohuwar ajiya).

Gwamnatin Tarayya ta gindaya sharudda shidda da cika su ya waja a  kan makarantu a dukkan matakai kafin a sake bude su.

A ranar 19 ga watan Maris, 2020 ne gwamnatin ta rufe dukkan makarantu a kokarinta na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Karamin Ministan Lafiya Chukwuemeka Nwajiuba ya ce kafin a sake bude makarantu dole ne kowace makaranta ta samar da wadannan abubuwa:

  1. Samar da kayayyakin wanke hannu.
  2. Auna zafin jiki.
  3. Kashe kwayoyin cuta a daukacin jiki a dukkannin kofofin shiga azuzuwa, ofisoshi, dakunan kwanan dalibai da sauransu.
  4. Kashe kwayoyin cuta a ko ina a fadin makarantar.
  5. A yi iya kokari wurin tabbatar da kula da kuma kare lafiya.
  6. Tabbatar da bayar da kariya a azuzuwa da ofisoshi da zauran wurare.

Duk da haka Ministan ya gargadi makarantu da su guji budewa ba tare da samun izinin yin hakan daga Gwamnatin Tarayya ba.

“Yayin da muke kokarin sassauta dokar kulle da zai kai ga bude makarantu, ina kira ga dukkan shugabannin makarantu kada su jira sai an sanar da sake bude makarantu kafin su ce za su dauki matakan da suka dace na bin ka’idodi da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta shimfida.”

A ranar Talata ne Aminiya ta ruwaito yadda jam’ian hukumar NCDC suka hana dalibai komawa makaranta a jihar Kuros Riba.

A makon jiya ne Gwamna Ben Ayade ya bukaci a bude makarantu uku a mazabun ‘yan majalisar tarayya uku da ke jihar a matsayin gwaji.

Jihar Kuros Riba ita ce kadai kawo yanzu ba a samu bullar cutar coronavirus ba fadin Najeriya.