Gwamnati ta fito da Abinci ta tallafawa Talakawa – Sarkin Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yi kira ga Gwamnatocin kasar nan, da su fitar da kayan abincin da suka ajiye su rabawa talakawa domin rage radadin mawuyacin halin da suke fama da shi, na rashin abinci. Sarkin ya yi wannan kira ne, a lokacin da ya ke […]

Gwamnati ta fito da Abinci ta tallafawa Talakawa – Sarkin Saminaka

Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yi kira ga Gwamnatocin kasar nan, da su fitar da kayan abincin da suka ajiye su rabawa talakawa domin rage radadin mawuyacin halin da suke fama da shi, na rashin abinci.

Sarkin ya yi wannan kira ne, a lokacin da ya ke jawabi a wajen taron bikin Maulidi, da aka gudanar a garin Saminaka a ranar Alhamis.

Sarkin ya yi bayanin cewa daukar wannan mataki, ya zama wajibi ganin irin abin da ya faru a yan kwanakin nan, inda talakawa suka rika fasa wuraren da aka ajiye abinci a kasar nan.

Ya yaba wa al’ummar yankin Saminaka, kan yadda basu shiga wannan al’amari na fashe-fashen wuraren da aka ajiye, abinci ba.

Ya yi kira ga shugabannin addini, su cigaba da yin addu’o’i, domin  addu’a ce kadai magannin dukkan matsalolin da suke damun mu, a kasar nan.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa