Gwamnati ta haɗa kai da kamfanoni don yaƙar ɗumamar yanayi

Gwamnatin ta jaddada aniyar yaƙi da duk abin da zai haifar da ɗumamar yanayi.

Gwamnati ta haɗa kai da kamfanoni don yaƙar ɗumamar yanayi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ci gaba da haɗa kai da kamfanoni masu zanan kansu wajen yaƙi da ɗumamar yanayi a faɗin ƙasar nan.

Ƙaramin Ministan Muhalli, Dokta Iziaq Adekunle Salako ne, ya bayyana hakan a wajen bikin buɗe Kamfanin makamashi na Atmosfair Climate and Sustainability Limited, wanda ya samar da wani rishon girki mai aiki da gawayi.

A cewar ministan, ma’aikatar muhalli tana da wajen ciyar da duk wasu shirye-shirye da suke da suka yi daidai da tsare-tsaren wannan Gwamnatin ta fi bai wa muhimmanci.

Ministan, ya yaba wa ƙoƙarin kamfanin wajen inganta harkar girki ta hanyar sanar da murhun nagartacce don samar da lafiyayyar al’umma da kuma tsaftataccen muhalli.

“Kokarin da kuka yi na ɓullo da wannan harkar ƙere-ƙere abu ne da zai kawo sauyi a rayuwar al’ummar Najeriya.”

Ministan, ya yi kira ga kamfanin da ya sauƙaƙa kayan da yake sarrafawa don al’ummar ƙasar nan su iya saye cikin sauƙi.

Da yake nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Muhalli na jihar, Nasiru Sule Garo, ya wakilta ya bayyana ɗumamar yanayi a matsayin abin da ya damu duniya don haka ya ce duk wani yunƙuri na rage sare bishiyu abu ne da zai haifar da ɗa mai ido.

Ya shawarci ’yan kasuwa da su sanya jarinsu a duk wata harkar da ta yaƙi sha’anin ɗumamar yanayi, inda ya ƙara da cewa gwamnati za ta samar da duk wani taimako wajen ganin an kai ga samun kyakkyawan sakamako.

A jawabinsa na maraba tun da farko, Darakta Hulda da Gwamnati na Kamfanin Atmosfair, Alhaji Abdurrahman Sulaiman Bawa, ya bayyana cewa ƙoƙarin da suke yi a Najeriya ya wuce batun samar da kayayyaki.

“Mun gudanar da gangamin wayar da kai a jihohi tara a faɗin ƙasar nan, inda muka samu damar ganawa da dubban magidanta. Zuwa yanzu da muka fara mun sayar da fiye da rishon girki dubu 30.”

Ya kuma ƙara da cewa sakamakon yarda da tasirin haɗin gwiwa da suka yi, ya sa suka haɗa kai da cibiyoyin gudanar da bincike game da yadda za su mayar da sharar gona ta zama wani abu da zai zama madadin yin amfani da fetur.

Aminiya ta rawaito cewa Ministan Muhalli, ya kai makamanciyar wannan ziyarar kamfanin Burn manufacturing company da ke yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, inda ya duba irin ayyukan da suke yi na samar da murhun girki.