Gwamnati ta hada kai da mafarauta a yaki barayin shanu
Shugaban Najeriya Mahammadu Buhari a cikin watan Augusta ya kaddamar da farautar barayin shanu da ‘’yan fashi da makami da suka addabi kasar nan. Wadancan masu miyagun halaye da na zayyana a wasikata saboda haka naga ya dace in bai wa shugaba Buhari shawara idan ’yana son al amarin ya yi nasara akwai bukatar a […]
Shugaban Najeriya Mahammadu Buhari a cikin watan Augusta ya kaddamar da farautar barayin shanu da ‘’yan fashi da makami da suka addabi kasar nan. Wadancan masu miyagun halaye da na zayyana a wasikata saboda haka naga ya dace in bai wa shugaba Buhari shawara idan ’yana son al amarin ya yi nasara akwai bukatar a ce gwamnatin tarayya ta hada kai da mafarauta, domin a ganina za su taimaka wajen damke wadanda suka zama marasa gaskiya a Najeriya, tunda mafiya yawan mafarauta a kasar nan suna da taimako, wato lakani na asiri, wanda idan za a yi amfani da su za su iya shiga wajen da jami’an tsaro ba za su iya shiga ba. Mafarauta irin su Alhaji Ali kwara Azare suna da masaniya a kan dazukan kasar nan da duk wani loko da sako na kasar nan. Kuma duk Najeriya kowa ya sans . Sanin kowa ne suna taimaka wa ana samun nasara wajen yaki da marasa gaskiya.
Akan batun masu satar shanu da satar mutane kuwa, kimanin shekara 15 a baya babu wani batu makamancin haka a nan Areawacin Najeriya, sai dai kawai mu rika jin labarai sabanin yanzu da satar mutane da garkuwa da mutane take neman zama ruwan dare a Areawacin kasar nan. Ina shawartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bai wa bangaren tsaro muhimmanci kamar dai yadda ya fara da nufin magance barazanar da ’yan ta adda suke yi wa al’umma a Areawacin kasar nan da ma fadin kasar gaba daya.
A kwai bukatar a hada karfi da mafarauta wajen taimaka wa gwamnatin tarayya su zakulo mutane masu irin wannan mummunan aiki a cikin jama’a. Sau da yawa idan mafarauta suka kama irin wadannan mutane ana samunsu da shaida mai kwari da ta hada da bindigogi da muggan makamai da suke tabbatar wa ’yan ta’adda ne. Don haka ya kamata a ce gwamnatin tarayya ta taimaka wa mafarautan. Kuma akwai bukatar gwamnatin ta yi wata doka da za ta sa a rika mayar wa wadanda aka saci dukiyarsu, wajensu cikin hanzari su kuma barayin a dauki matakin hukunci a kansu cikin sauri. Wallahi duk Najeriya Alhaji Ali kwara ya ciri tuta wajen taimaka wa jama a da gwamnati wajen hana barayi sakat a fadin Najeriya. Saboda haka ne ma gwamnatocin Bauchi da Jihar Jigawa suka karrama Alhaji Ali kwara da lambar yabo ta zinare.
Editan Aminiya ku da sauran kafafen yada labarai kuna da gudunmuwar da za ku bayar. Don haka ina fatan Allah ya kara wa jaridar Aminiya farin jini ya kuma kareku daga sharrin abokan adawa da kokarin fito da gaskiya fili komai dacinta. Amin.
Sani Garba ya rubuto makalarsa daga birnin Dutse , Jihar Jigawa.
Lambar waya 08036528835