Gwamnati ta hamta hakar ma’adanai a Zamfara
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da hakar ma’adanai a Jihar Zamfara sanadiyyar kisan gillar da ‘yan bindiga ke yi wa jama’a a fadin jihar. Sanarwar ta fito ne daga bakin Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu, a jiya Lahadi. IGP Adamu, ya bayyana haka ne a taron jami`an tsaro da aka yi […]
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da hakar ma’adanai a Jihar Zamfara sanadiyyar kisan gillar da ‘yan bindiga
ke yi wa jama’a a fadin jihar.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu, a jiya Lahadi.
IGP Adamu, ya bayyana haka ne a taron jami`an tsaro da aka yi a ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari.