Gwamnati ta hana mu kamo masu satar mutane a daji —Mafarauta
Mafarauta sun zargi gwamnati da hana su kutsawa cikin dazukan jihar domin kamo masu garkuwa da mutane a Jihar Oyo.
Mafarauta sun zargi gwamnati da hana su kutsawa cikin dazukan jihar domin kamo masu satar mutane a Jihar Oyo.
Shugaban Kungiyar Mafarauta ta Soludero a jihar, Oba Nureni Akintola Anabi, ya ce kungiyar ta dade tana neman gwamnatin jihar Oyo da Sufeto-Janar na ’yan sanda Kayode Egbetokun, su ba ta iznin shiga cikin dazukan jihar domin kamo masu satar mutane, amma har yanzu ba a ba ta ba.
Ya ce idan mahukumta suka ba su dama to za su shiga cikin dazukan su kamo masu satar mutane tare da mika su ga jami’an tsaro.
Amma ya ce duk da cewa “’ya’yan kungiyar ne suka san ciki da wajen dazukan jihar, amma ba a ba su izinin yin aikin ba.
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Fitattun ’Yan Soshiyal Midiya Wajen Sauya Ra’ayin Al’umma
- An sassauta dokar hana fita a Kaduna da Zariya
“Idan muka yi gaban kanmu muka shiga cikin dazukan mahukumta suna iya neman dalilin da ya sa muka dauki matakin yin hakan.
“Shi ne dalilin da ya sa muka dakata“, inji Shugaban Mafarautan.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Oyom Adewale Osifeso, sai dai bai amsa kiran wayar wakilinmu ba.
Shugaban kungiyar mafarautan ta yi wanna zargi ne dai bayan tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Asimiyu Alarape, ya ja hankalin matafiya a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Oyo su yi hattara saboda masu satar mutane suna yin badda-kama a matsayin fasinjoji a kan hanyar suna garkuwa da mutane.
Ya bayar da shawarar ne a Ibadan bayan wani makwabcinsa ya fada hannun masu satar mutane a lokacin da ya shiga motar bas tare da wasu mutane a kan hanyar zuwa Oyo daga Ibadan.
Alarape ya ce yanzu dazukan da ke kan wannan hanya ta Express ta zama mafakar masu satar mutane da garkuwa da su a Jihar Oyo.
Ya ce makwabcin nasa ya shaida masa cewa ya shiga wata motar bas tare da wasu mutane a kan hanyar zuwa Oyo daga Ibadan inda direban motar ya taka birki ya tsaya cikin daji da sunan sauke fasinja.
A nan ne mutanen da direban motar suka ingiza keyar fasinjoji takwas cikin daji.
Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin ya ce mutanen sun sallamo shi tare da wasu fasinjoji biyu amma sun ci gaba da yin garkuwa da sauran mutane biyar.
Ya nemi rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta dauki tsauraran matakan tsaro a kan wannan hanya.