Gwamnati ta haramta wa makiyaya shiga Jihar Gombe

Idan aka bari makiyaya suka shigo za su yi barna.

Gwamnati ta haramta wa makiyaya shiga Jihar Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya

Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar da ta haramta wa makiyaya da ke waje shiga cikin jihar sai bayan watan Janairu na badi.

Gwamnatin ta dauki matakin ne da nufin hana rikicin da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya a kowace shekara, wanda ke haddasa asarar rayuka da dukiya.

Kwamishinan Tsaro na Jihar, Adamu Dishi Kupto, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar kuma ta hana kiwon dare, lokacin da ya ce aka fi yin barna da kuma hana wa yara kanana kiwo.

“A yanzu manoma ba su kwashe amfanin gonarsu ba, idan aka bari makiyaya suka shigo za su yi barna, dalilin da ya sa gwamnati ta kafa dokar kenan,” in ji shi.

‘Rikicin makiyaya da manoma manufa ce ta raba kan ’yan Arewa’

A watan Maris ne Tsohon Gwamnan Jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ana fakewa da sunan rikicin makiyaya domin a raba kan al’umma a kasar nan.

Sanata Abdullahi wanda ke zaman dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Nassarawa ta Yamma, ya bayyana hakan ne yayin wata hirarsa da manema labarai, inda ya ce ana kokarin raba kan Hausawa da Fulani da sunan rikicin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya.

A hirar tasa, ya ce ana fakewa ne da sunan hare-haren da ake zargi makiyaya na kai wa wasu jihohin kasar da manufar raba kan al’ummar yankin.

A cewarsa, rikicin makiyaya ya samo asali ne sakamakon cinye hanyoyi da burtalai da sauran dazukan da aka kebe musamman domin makiyaya, sannan an gaza sama da wani tsari da zai ba su damar ci gaba da gudanar da harkokinsu.

“Ana neman dalili ne domin bata sunan makiyaya don a la’ance su, idan aka zo maganar kiwo wa yake wani batun Kudu? Sanin kowa ne cewa kiwo a Arewa yake, saboda haka wuta ce ake kunnowa don ganin ana raba kan al’ummar Arewa,” in ji shi.

Sanatan ya ce akwai bukatar gwamnati ta kawo karshen wannan matsala ta hanyar fahimtar barazanar da ke tattare da yadda ake kiwo barkatai ba tare da wani kyakkyawan tanadi ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta samar wa makiyaya wata hana da za su rika gudanar da harkokinsu ba tare da sun shiga hakki ko ketare iyakar al’umma ba.

“Dole ne mu so juna, don mutumin Kudu bai san wata kabila Hausa Fulani ba, a ganinsa duk a dunkule muke, saboda haka yanzu kuma so ake a raba kan Hausawa da Fulani,” a cewarsa.