Gwamnati ta janye karar da ta kai Muhammad Abacha

A shekaranjiya Laraba ce Gwamnatin Tarayya ta janye karar cin hanci da rashawa a kan Mohammad Abacha, dan tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha.Lauyan Gwamnati ya bayyana wa kotu cewa, Ministan Shari’a Muhammad Adoke ne ya umarce shi ya janye karar. Gwamnati ta zargi Muhamamd Abacha da karbar kadarar sata da kimarta ya kai Naira […]

Gwamnati ta janye karar da ta kai Muhammad Abacha
Gwamnati ta janye karar da ta kai Muhammad Abacha

A shekaranjiya Laraba ce Gwamnatin Tarayya ta janye karar cin hanci da rashawa a kan Mohammad Abacha, dan tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha.
Lauyan Gwamnati ya bayyana wa kotu cewa, Ministan Shari’a Muhammad Adoke ne ya umarce shi ya janye karar. Gwamnati ta zargi Muhamamd Abacha da karbar kadarar sata da kimarta ya kai Naira biliyan 100 da miliyan 380, kudin da ake zargin mahaifinsa tsohon Shugaban kasa Janar Abacha, wanda ya yi mulki a tsakanin 1993 zuwa 1998 ya yi sama da fadi da su.
Lauyan Gwamnatin Tarayya, Daniel Enwelum ya bayyan bukatar janye karar a kan wanda ake zargi. Sannan ya gabatar da bukatar neman a daina yin wannan shari’a.
Lauya Enwelum ya ce bisa la’akari da wasu bayanai da wasu dalilai, ya zama dole su janye wannan kara. Sai dai bai bayyana wadannan dalilai da suka sanya aka janye karar ba.
Kakakin Ministan Shari’a, Ambrose Momoh da aka tuntube shi, ya ce, ba ya cikin ofis, kuma shugabansa, Mista Muhammad Adoke zai iya bayyana wadannan dalilai.
Kotun ta sallami Muhammad, kuma alkali ya amsa bukatar daina ci gaba tuhumar, al’amarin da lauyan wanda ake kara, Abdullahi Haruna ya amince da shi.
Tuni aka dawo da dimbin dukiyar da ake zargin Shugaba Abacha da boyewa a kasashen duniya da ta kai Dala miliyan 500 (kimanin Naira biliyan 83), bayan da gwamnatin Amurka ta tsare dukiyarsa.
Mukaddashin Lauyan Gwwmnatin Amurka, Mytyhili Raman da Mataimakiyar Darakta a Hukumar Shari’a, sashin kula da manyan laifuffuka, balerie Parlabe ta hukumar binciken asiri ta FBI sun bayyana matsayin gwamnatinsu, inda suka ce dukiyar da Abacha ya sace da wuya a samu wanda ya taba yin irinta a cikin tarihi, musamman in aka yi la’akari da cewa miliyoyin ’yan Najeriya na fama da talauci.
Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta yi nuni da munin bakin mulkin Abacha, amma makonnin da suka wuce ta karrama shi a matsayin jagora, wajen “hadin kan al’umma da kishin kasa da ci gabanta.” Shugaba Abacha na cikin jerin mutum 100 da aka karrama a wajen bikin cikar Najeriya shekara 100.