Gwamnati ta janye karar da ta shigar da ’yan kwadago

A yanzu kuma shawara ta rage wa shugabannin ’yan kwadagon kan janye zanga-zangar.

Gwamnati ta janye karar da ta shigar da ’yan kwadago

Zanga-zangar NLC

Gwamnatin Tarayya ta janye karar da ta shigar da shugabannin Kungiyar Kwadago a kotu saboda zanga-zangar da suka jagoranta a fadin Najeriya kan tsare-tsaren gwamnatin da suke zargin sun jefa ’yan kasar a cikin halin -ni-’yasu.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata wasika da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta aike wa lauyan ’yan kwadagon, Femi Falana.

Femi Falana ya ce a yanzu kuma shawara ta rage wa shugabannin ’yan kwadagon kan janye zanga-zangar ko akasin haka.

Martanin NLC bayan maka ta a Kotu

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a makon jiya ne Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce an kawo musu sammacin kotun da cewa zanga-zangar da suka gudanar a ranar Laraba raini ne ga umarnin kotu.

Sai dai ya ce za su amsa kiran kotun amma hakan ba zai hana su gwagwarmayar sama wa al’ummar kasa sauki ba.

“Ana zarginmu da raina kotu, don haka muna kira ga ’yan Najeriya da su farga,” in ji Mista Ajaero, wanda a safiyar Larabar ya jagoranci masu zanga-zangar tare da takwaransa na kungiyar ma’aikata ta TUC, Festus Osifo, zuwa Majalisar Dokoki ta kasa inda suka mika takarar kokensu ga gwamnati.

A cewarsa, za su ci gaba da jiran matakin da gwamnati za ta dauka kan bukatun da kungiyoyin suka gabatar mata ta hannun majalisa, wadda ta ba su tabbacin gwamnati za ta yi abin da ya kamata.

A Yammacin Larabar da ta gabata ne kuma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin kwadagon a fadar gwamnati da ke Abuja.

’Yan kwadago sun dakatar da zanga-zanga

Bayan gawanar ce kungiyoyin kwadagon suka sanar da dakatar da da zanga-zangar domin ba wa gwamnati damar cika alkawuran da ta daukar wa ’yan Najeriya.

Ajaero ya shaida wa ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa cewa bayan tattaunawar, sun amince su ba gwamnatin karin lokaci domin ganin kamun ludayinta.

A cewarsa, “Babbar nasarar da zanga-zangarmu ta samu ita ce bukatar Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ta tattaunawa da NLC da TUC a sirrance.

“Mun tattauna kan muhimman abubuwan da suka taso bayan janye tallafi, kuma ya tabbatar mana da cewa za a farfado da matatar man fetur ta Fatakwal kuma za ta fara aiki nan da watan Disamba.

“Ya yi mana alkawarin cewa nan ba da dadewa ba za a kara wa ma’aikata mafi karancin albashi.

“Muna godiya ga ’yan Najeriya kuma za mu ci gaba da jiran gwamnati mu ga kamun ludayinta wajen cika nata alkawuran da Shugaban Kasa ya yi,” in ji Shugaban na NLC.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano