Gwamnati ta kafa dakarun kare albarkatun noma
Gwamnatin Tarayya ta kafa jami’an tsaro na musamman da za su rika ba da kariya ga dukiyar da aka zuba a bangaren harkokin noman kasar. Dakarun za su rika yaki da satar shanu da rikicin manoma da makiyaya da ke aukuwa a sassa da dama na kasar. Matimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi bayyanin […]
Gwamnatin Tarayya ta kafa jami’an tsaro na musamman da za su rika ba da kariya ga dukiyar da aka zuba a bangaren harkokin noman kasar.
Dakarun za su rika yaki da satar shanu da rikicin manoma da makiyaya da ke aukuwa a sassa da dama na kasar.
Matimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi bayyanin a taron kwanaki uku da aka yi kan yadda za a farfado da kamfanonin bunkasa kiwo wanda aka gudanar a Abuja, jiya.
Osinbajo wanda Ministan Albarkatun Noma, Dokta Audu Ogbeh, ya bayyana cewa tuni gwamnati ta bayar da horo ga dakaru dubu uku don magance satar shanu tare da kare albarkatun noma.