Gwamnati ta kafa kwamitin magance rikicin manoma da makiyaya

Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti domin samo hanyoyin magance rikice-rikicen da ke yawan aukuwa a tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.Kwamitin yana karkashin shugabancin Babban-Daraktan Makarantar Koyar da Dabarun Zaman Lafiya da Sasanci (IPCR), Farfesa Oshita O. Oshita ne.Wata takarda da Mukaddashin Babban-Sakatare a Ma’aikatar Cikin Gida, Alhaji Muhammadu Maccido ya sanya wa […]

Gwamnati ta kafa kwamitin magance rikicin manoma da makiyaya
Gwamnati ta kafa kwamitin magance rikicin manoma da makiyaya

Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti domin samo hanyoyin magance rikice-rikicen da ke yawan aukuwa a tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.
Kwamitin yana karkashin shugabancin Babban-Daraktan Makarantar Koyar da Dabarun Zaman Lafiya da Sasanci (IPCR), Farfesa Oshita O. Oshita ne.
Wata takarda da Mukaddashin Babban-Sakatare a Ma’aikatar Cikin Gida, Alhaji Muhammadu Maccido ya sanya wa hannu, ta ce kwamitin zai fito da tsare-tsare da hanyoyin da za a shawo kan lamarin rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, inda za a tsara wani babban taro na masu ruwa-da-tsaki domin samar da mafita.
Takardar ta ce a yayin taron, akwai yiwuwar a fitar da tsari da hikimomin da masu ruwa-da-tsaki za su samar ta hanyar tattaunawa, kan yadda za a magance rashin jituwa a tsakanin manoma da makiyaya. Za a tattauna domin gano matsalolin da suke haifar da al’amarin da kuma maganinsu. Haka kuma tattaunawar za ta duba yadda al’amarin yake a nahiyoyi da kasashen duniya, tare da duba dokokin kasashen duniya da suka danganci al’amarin.
A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin, Oshita ya ce samar da wannan kwamiti ya nuna kyakkyawar niyyar wannan gwamnati, wajen samar da zaman lafiya da lumana a tsakanin al’ummar kasar nan. Ya ce, ya kamata kowane dan kasa ya ba da gudunmawar da ta kamata, sannan ya ba da goyon baya ga gwamnati domin bunkasa kasar nan.