Gwamnati ta mayar da mawakan Hausa gugar yasa – Shehu Ajilo

Alhaji Shehu Ajilo danguzuri mawakin Hausa ne da ya dade ana damawa shi a harkar waka. Aminiya ta yi kicibis da shi ne a wajen wani taron mawakan Hausa da aka gudanar a Kaduna kwanakin baya, inda ta zanta da shi a kan sana’rsa ta waka da kuma bambancinsu da mawakan zamani.  Ga kuma yadda […]

Gwamnati ta mayar da mawakan Hausa gugar yasa – Shehu Ajilo
Gwamnati ta mayar da mawakan Hausa gugar yasa – Shehu Ajilo

Alhaji Shehu Ajilo danguzuri mawakin Hausa ne da ya dade ana damawa shi a harkar waka. Aminiya ta yi kicibis da shi ne a wajen wani taron mawakan Hausa da aka gudanar a Kaduna kwanakin baya, inda ta zanta da shi a kan sana’rsa ta waka da kuma bambancinsu da mawakan zamani.  Ga kuma yadda hirar ta kasance:

Me za ka ce game da wannan rana ta Mawakan Hausa?

Gaskiya na yi farin ciki da wannan rana da wadanda suka shirya wannan taro da kuma ku da kuka samu damar ziyartar mu, domin ku tallata al’amuranmu, domin gwamnati ta san ko mu su waye da kuma irin gudunmuwar da muke bayarwa, wanda ita ba ta ba mu. Domin yau idan yaki ya tashi, sai ka ji sun ce ina mawaka, su yi mana wakar zaman lafiya.
Idan suna ya tashi za a ce mawaka, in wa’azi za a yi sai a ce mawaka, komai za a yi mawaka. Saboda haka ni wannan rana ta yi mini dadin gaske, domin gwamnati ta san da zaman mawakan Ibo da na Yarbawa da na Tibi da na sauran kabilu amma mu mawakan Hausa ba a san da mu ba, musamman mu mawakan da, da ake damawa da mu har yanzu. An shuka mu a kasa, an bi an taka mu, ba a neman mu sai idan ta baci, sai ka ji an ce ku zo ku taimaka da wakar zaman lafiya. Idan kuma an gama sai a mayar da kai gugar yasa. Watan a debo kasar da kai, ba a wanke ba. Wannan shi ke ci mana tuwo a kwarya.
Ko akwai wani bambanci tsakanin wakokin da da kuma na zamanin yanzu?
Akwai, domin idan ka duba wakokin ’yan zamanin yanzu, misali kai din nan da nake kallon ka kamar Bahaushe ne tsantsa amma an tauye maka al’adunka saboda ni kaina din nan akwai wanda ya taba cewa da ni in koma yin amfani da Fiyano na zamani. Na ce da shi Allah Ya sauwake, ai gara in mutu. To, me kuma nake nema wanda tun zamanin Sardauna nake waka?
Tun ana yawo da ni ana cewa aljanin kida har Allah Ya kawo ni wannan lokaci, to, me kuma nake nema? Baya ga haka kuma, in ga jikata na rawa a gabana sannan ni kuma in saka rabin wando yadda suke yi, Allah Ya hana ni. Ko in dauko yarinya jikar-jikata, wadda kila na haifi mahaifiyarta, kila a ce na koma can ai ta baci.
Mu dai ka bar mu idan kana son ganin ranarmu, a ce ana nadin sarauta ko kuma wata gasa. Ko a jaye kake ka ce a yi ma sirdi, waka ko amfanin ka ce a nan take za ka gane cewa lallai an zubar da al’adu.
Idan kayi la’akari mawakan yanzu sukan dauki lokaci mai tsawo kafin su rubuta waka amma kuma mawakan da irin ku, kukan kalli abu ne a yanzu ku wake shi.
Ai’ Allah Ya gafarta Malam, a yanzu babu fasaha domin idan ka dubi wakokin yanzu, kusan duk kidan fiyanon iri daya ne. Amma mu idan yau zan dauki wakar mahauci, kidana daban ne. Idan kuma na dauki wakar manoma, kidana daidai zai yi da na manoma. Haka nan idan na shiga fada, nan ma kidana sai ya canza. Na san me zan fada maka idan kai sarki ne kuma sarki wa mahaifinka ya gada sannan wani sarki mahaifinka ya gada, dole tsigarka ta tashi.
Akwai wata mata Jakadiya da na taba yi wa waka, inda na rika fadin sunayen sarakunan da suka shude, suka koma ga Allah a zamanin baya, wanda abu ne mai wuya mawakan yanzu su iya hakan. Ko an rubuta sai an je an yi bita (rehearsal). Na tuna a lokacin zaben 12 ga Yuni, lokacin kasar nan na tangal-tangal sai aka neme mu a Bauchi cewa mu yi waka.
Duk mawakan wannan lokaci an tara mu a Bauchi har gwamnanmu ya ce da ni, Ajilo an ce da kai a je bayan gari domin yin rihasal ka ce ba za ka ba. Na ce masa e! Saboda ita waka ba a yi mata rihasal. Idan ya zo iyakacin in fada wa na baya cewa ya rika dubar kafata kawai. Domin wani lokacin sai bayan an je an yi rehasal sai a zo fili wakar ta baci, ka ga ke nan na kunyata kaina a gaban jama’a da kuma ku.
Saboda haka sai na tanbaye shi da ya fada mini taron ko a kan mene ne, sai ya ce a kan zaman lafiya. To, da aka kirawo ni gaban jama’a sai na rera wakar nan ‘Allah Wahidin Ka Taimaki ’Yan Najeriya kasarmu Ta Zauna Lafiya A Fahimci Juna.’ Kuma Allah Ya taimake mu wannan waka ta ciwo wa Jihar Kaduna zinari da sauran kyaututtuka. Kai dama wakar aka rufe taron a wannan lokaci. Ka ga da a ce gwamnatin Najeriya tana taimakon mutane irinmu ne da yanzu wallahi mun zama wani abu.
Na yi wakoki a kan zaman lafiya, na yi a kan noma domin kullum za ka rika jin a gidajen radiyo cewa jama’a su koma noma. Na kuma yi waka a kan tattalin arziki. Na yi a kan a rika tausaya wa talaka. Na kuma yi a kan mutum sai Allah. In da a kasashen waje nake da kila mai son gani na ma sai ya cike fom.
Ga alama dai ka samu alheri da waka, haka ne?
Alhamdulillah, kwarai kuwa amma sai dai ba a gwamnati ba. A biki, kauyuka, gidan suna da sauransu. A yanzu haka ma ina da wasanni kusan hudu a hannuna. A can kauyuka wani ma sai ya nemi ya takani saboda kawai yana san ga rigarsa ga ta Ajilo.
Idan kuma a gwamnatance kake magana, gaskiya babu shakka ina da ubangida daya tankar dubu, wato tsohon Gwamnar Jihar Kaduna, Senata Ahmed Muhammad Makarfi. Babu abin da dan nan bai yi mini ba. Ya sanya ni cikin shugabanin zartaswa na gidan Radiyon Kaduna na farkon shekaru hudunsa na mulki. Bayan na kammala lafiya sai ya ba ni kudi da na ga sun amsa kudi sai na taso daga kauyenmu da iyalina muka dawo unguwar Kanawa na sayi gida muna zaune.
Har gobe duk Azumi ko Sallah ko kuma idan na ziyarce shi a ranar Lahadi da mun gaisa za ka ga na dawo da dan dauri mai matsakaicin nauyi daidai gwargwadon na cin abinci.
Yanzu wasu jama’a na kokawa da wakokin zamani da cewa suna bata tarbiyar matasa. Ya kake ganin wannan abu?
Kamar yadda na fada maka ne cewa, ni yanzu ba zan iya saka wando rabin duwawu ba in fito ina rawa da mutuncina. Su a wurinsu sun ce suna gyara tarbiyya ne, mu kuma a wajenmu muna ganin wasu yaran suna lalacewa. Saboda haka babu abin da zan ce, domin kowa da yadda Allah Ya yi zai ci abinci. Kila ni da dadewa kake jin wakokina a gidajen rediyo.
Amma a yau an wayi gari babu gidan da babu maroki saboda an lura cewa yau mu ke sanya manyan riguna da hawa manyan motoci. Mu ke kuma auren mata bula-bula. Sannan kuma ’yan Nairan nan ba mu rasa ta.
Wace shawara ke gare ka ga mawaka?
Idan kai bai wa Bamaguje Alkur’ani ka yi ridda saboda haka ni ban san komai game da mawakan zamani ba amma idan ta bangarenmu ne zan je, domin ai ga shi taro ake yi na hadin kai, wanda mu ya kamata a ce muna da wannan kungiya tun a shekarun baya.
Shi ya sa wannan bawan Allah ALA yakan ziyarce ni har gidana mu gaisa, wani lokaci har kauyenmu yana zuwa neman shawarata. Yakan ce da ni mu ne iyayensu. Shi ya sa nake kaunarsa kamar yadda nake kaunar dana na cikina. Don an ce ko ba ka da wayo ka so mai son ka.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa