Gwamnati ta miƙa tayin N62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnonin Nijeriya sun sanar da cewa ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Gwamnati ta miƙa tayin N62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

‘Yan kwadago

Gwamnatin Tarayya ta yi wa ƙungiyoyin ƙwadago tayin ba su naira 62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi maimakon naira 60,000 da ta yi musu tayi tun da farko.

Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya George Akume ne ya bayyana haka ranar Juma’a da daddare a taron da ya jagoranci sauran manyan jami’an gwamnati da ɓangarori masu zaman kansu.

Ya ce za su miƙa wa Shugaba Bola Tinubu wannan shawara domin ya aike wa majalisun dokokin ƙasar don su mayar da ita doka.

Hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon sa’o’i ɓangarorin biyu suna tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin.

A nata ɓangare, ƙungiyar ƙwadagon ta rage buri zuwa naira 250,000, saɓanin naira 494,000 da a baya ta dage cewa dole gwamnati ta biya.

A farkon makon nan ne gwamnatin ƙasar ta buƙaci ƙungiyar ƙwadagon ta janye yajin aikin da ta fara, bayan da gwamnatin ta alƙawarta yin ƙari kan naira 60,000 da ta yi a makon da ya gabata.

To amma tuni ƙungiyar gwamnonin Nijeriya ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta ce gwamnonin jihohin ƙasar ba za su iya biyan naira 60,000 ɗin da gwamnatin tarayyar ta yi tayin biyan ma’aikatan tun da farko ba.

Kawo yanzu dai ɓangarorin biyu sun tashi zaman ba tare da cimma matsaya ba, sai dai sun alƙawarta ci gaba da tattaunawar domin samun daidaito.

To sai dai ba a sani ba ko wannan motsi da duka ɓangarorin suka yi ka iya sa a cimma matsaya, don kauce wa komawa yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon za su iya shiga, lamarin da masana ke cewa zai iya haifar wa tattalin arzikin ƙasar koma baya.