Gwamnati ta musanta bai wa kamfanin bogi kwangilar titin Kano zuwa Abuja
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana rahoton a matsayin abin takaici da ka iya dulmuyar da jama’a.
Gwamnatin Tarayya ta musanta bai wa kamfanin bogi kwangilar ƙarasa aikin titin Kano zuwa Abuja.
Gwamnatin ta kuma soki rahoton da aka buga a jaridar Daily Trust a ranar 21 ga watan Janairu, wanda ya yi iƙirarin cewa ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta bayar da kwangilar gyaran wani sashen titin Abuja zuwa Kano ga wani kamfani mai suna Infoquest Nigeria Ltd, wanda aka gano cewa ya daina aiki.
Sai dai a wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata a Abuja, Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana rahoton a matsayin abin takaici da ka iya dulmuyar da jama’a.
Ministan ya bayyana cewa kamfanin Infoquest Nigeria Ltd ya samu kwangilar naira biliyan 252.89 daga hukumar kula da kadarorin gwamnati (BPP) domin gyara wani ɓangare na hanyar da ta tashi daga Abuja zuwa Kaduna ta zarce zuwa Zaria da Kano.
Ya bayyana cewa ma’aikatar ba ta da wata alaƙa ta kasuwanci da kamfanin Infoquest Nigeria Ltd.
Ya kuma ƙara da cewa kamfanin da ke da alaƙar kwangila da ma’aikatar a kan aikin hanyar shi ne Infiouest International Limited kuma kamfanin yana aiki.
Kazalika, Ministan ya ce kamfanin da aka bai wa kwangilar ya cika duka sharuɗɗan da ake buƙata a ƙarƙashin dokar kamfanoni na ƙasa.
Dangane da hakan ne Ministan ya buƙaci jaridar Daily Trust ta nemi afuwar jama’a da kuma ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta hanyar buga sanarwar a cikin aƙalla jaridu biyar na ƙasar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a kwanakin baya ne Gwamantin Tarayya ta ƙwace kwangilar daga hannun Kamfanin Julius Berger saboda rashin daidaitawa kan farashi.
Sai dai a wata sanarwa da kamfanin Julius Berger ya wallafa a manyan jaridun Najeriya, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar darajar Naira sun haifar da tashin farashin makamashi da kayan aiki.
Sanarwar ta kara da cewa duk da alƙawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na ba kamfanin Naira biliyan 20 a duk wata domin kammala aikin cikin watanni 14, gwamnatin ba ta bashi ko sisi ba tun daga watan Nuwambar 2023.