Gwamnati ta musanta mutuwar mutum 200 sanadiyar bakuwar cuta a Yobe

Ana gargaɗin jama’a da su ci gaba da shan ruwa akai-akai kamar aƙalla lita 3-4 a kullum.

Gwamnati ta musanta mutuwar mutum 200 sanadiyar bakuwar cuta a Yobe

Gwamnatin Yobe ta ƙaryata rahotanni da ke cewa wata baƙuwar cuta ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 200 a wasu ƙananan hukumomin jihar.

A bayan nan ne wasu kafofin watsa labarai suka wallafa cewa a cikin makonni biyu kacal, an samu wasu cututtuka da ba a gane kansu ba da suka yi ajalin aƙalla mutum 200 a kananan hukumomin Potiskum da Nangere da ke jihar.

Sai dai Kwamishinan Lafiya na Jihar Yobe, Dokta Lawan Muhammad Gana ya karyata labaran a yayin tattaunawarsa da manema labarai a garin Damaturu.

Dokta Gana ya jaddada ƙarara cewar wannan labari da wasu marasa kishin kasa suka yaɗa shi a kafofin sadarwar zamani ba komai ba ne illa labari marar tushe da ba shi da ƙamshin gaskiya a ciki.

Kwamishinan ya ce bayan samun wannan labari na kanzon kurege  nan da nan ma’aikatarsa ta soma tuntubar manyan jami’an kula da ɓangarorin kiwon lafiya a matakin ƙananan hukumomi dangane da lamarin.

Dokta Gana ya ce binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewar babu ƙamshin gaskiya a ɓullar rahoton, hasalima ba su da masaniya kan yadda aka samo waɗannan alkaluman mamatan da ke yawo.

Ya ƙara da cewar, kan hakan ma’aikatarsu ta kula da kiwon lafiya ta ɗauki matakin faɗakar da al’umma dangane da yadda cututtuka ke saurin yaɗuwa a wannan lokaci na zafi

Ya ce an buƙaci jama’a da su riƙa kula da shan ruwa sosai da kuma rage kwanciya a cikin cunkoson jama’a sannan a tanadi buɗaɗɗen wuri yayin kwanciyar dare wanda iska za ta wadata.

Ya ƙara da cewa, a iya saninsa, “daga ranar 26 ga watan Disambar bara ta 2023 mun fara samun rahoton ɓullar cutar da ke da alaƙa da Sankarau wadda daga wancan lokacin zuwa yanzu mun samu adadin mutum kimanin 2,500 da suka kamu da ita.

“Sannan kuma a cikinsu mutane kimanin 85 ne suka rasu waɗanda su ɗin ma akasari sai da cutar ta ci ƙarfinsu sannan aka kai su asibiti yayin da wasu ma ko asibitin ba a kai su ba.

Ya ƙara da cewar “a bisa ga rahoton da jami’ansu suka kawo musu a cikin mako biyu da ake magana, an samu mutane biyu waɗanda suka rasu sakamakon wannan annoba ta sanƙarau amma ba mutane 200 ba kamar yadda wancan labari na jita-jita ya bayyana.

“Don haka mun tanadi jami’ai masu yawa da za su kula da wannan lamari cikinsu akwai jami’ai 200 da suka tanada don aikin shiga gidaje domin bincike da faɗakarwa.

“Akwai kuma jami’an sa-kai na al’umma sama da 1800 a Jihar Yobe da su ma ke wannan aiki kana akwai wasu jami’an da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da makamantansu.

Kwamishinan ya shawarci al’umma da cewar, da zarar sun ga alamar babba ko yaro sun fara kukan ciwon kai ko na wuya da makamantan su, su gaggauta zuwa wata cibiyar kiwon lafiya da ke kusa da su don ɗaukar matakin gaggawa a kai.

Ya kuma gargaɗi mutane da su guji yaɗa labarin da ba shi da tushe musamman kan abin da ya shafi wannan hali da ake ciki maimakon haka akwai buƙatar tuntubar wani jami’in kiwon lafiya don tabbatar da sahihin labari.

Dokta Gana ya kuma ba da tabbacin cewar, Gwamnatin Yobe karkashin Mai Mala Buni ta shirya tsaf domin inganta harkokin kiwon lafiya a tsakanin al’ummar jihar musamman yara.

Ya ce dangane da hakan ne suke ƙoƙarin ci gaba da samar da allurorin rigakafin wannan cuta ta Sanƙarau da dangoginta kyauta ga al’umma da a yanzu ma tuni shirye-shirye sun yi nisa.

Ya kuma sake gargaɗin jama’a da su ci gaba da shan ruwa akai-akai kamar aƙalla lita 3-4 a kullum a wannan yanayi da ake ciki na zafi wadda a bisa ga kiyasin masana, alƙaluman ma’aunin zafi na nuna ya kai kimanin kashi 45 maimakon 35 da shi ne yanayi mai dama-dama da ya kamata a ce ake da shi.