Gwamnati ta nanata kuduri inganta tsaro
Bayan hare-haren da ’yan Boko Haram suka kai a wasu yankunan Jihar Borno, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta. Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) ne ya bayyana haka a zantawa da wakilinmu a garin Maiduguri a ziyarar aikin wuni uku da ya kai […]
Ministan Tsaro Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya)
Bayan hare-haren da ’yan Boko Haram suka kai a wasu yankunan Jihar Borno, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummarta.
Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) ne ya bayyana haka a zantawa da wakilinmu a garin Maiduguri a ziyarar aikin wuni uku da ya kai garin Maiduguri.
Ministan Tsaron ya ce, “Yana daya daga cikin dalilin zuwana garin Maiduguri don in kara wa dakarunmu kwarin gwiwar tafiyar da wannan yaki da ya-ki-ci, ya-ki cinyewa, kuma ina da tabbacin cewa ba za ku ba ’yan Najeriya kunya ba domin hakki ne da ya rataya a wuyanmu mu ga cewa mun kare rayuka da dukiyoyin al’ummar wannan kasa. Don haka ina tabbatar muku cewa za mu iya kawar da ta’addanci a kasar nan. Hakan ya sa da na fara aiki na kai ziyara wuraren da rashin tsaro ya yi kamari kuma za mu magance su da yardar Allah.”
Janar Magashi ya ce za su tallafa wa sojojin yadda ya kamata musamman a bangarorin Arewa maso Gabas da Arewa ta Yamma wajen samar musu da ingantattu kuma yalwatattun kayayyakin aiki da ci gaba da koyar da su dabarun yaki da kuma ba su dukkan hakkokinsu na abin da ya danganci albashi a kan lokaci da alawus-alawus dinsu.
Ministan Tsaron ya yi kira ga mutanen Najeriya su kau da kai daga bambance-bambancen addini da siyasa da bangaranci da kabilanci, “Babu shakka nuna bambanci ke haifar da kiyayya a tsakanin al’ummar kasa har a kai ga daukar makamai ana kashe juna wanda kuma ba daidai ba ne,” inji shi.