Gwamnati ta nemi amincewar Majalisa don karbo bashin $1.2bn daga Brazil

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da bukatar neman sahalewar Majalisar Dokokin Tarayya don karbo bashin dala biliyan 1.2 daga kasar Brazil domin daukar nauyin shirye-shirye ayyukan noma da aka tsara a cikin kasafin kudin badi. Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan yayin da ta bayyana a gaban Kwamitin […]

Gwamnati ta nemi amincewar Majalisa don karbo bashin $1.2bn daga Brazil

Ministar Kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da bukatar neman sahalewar Majalisar Dokokin Tarayya don karbo bashin dala biliyan 1.2 daga kasar Brazil domin daukar nauyin shirye-shirye ayyukan noma da aka tsara a cikin kasafin kudin badi.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan yayin da ta bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kudi na Majalisar Wakilai a ranar Talata domin kare kasafin kudin da ma’aikatarta ta gabatar da hujja a kan kudin da ma’aikatar za ta bukata a badi.

Ministar ta ce Gwamnatin Tarayya ta aike wa da Majalisar Tarayyar bukatar karbo bashin daga kasar Brazil domin inganta ayyukan noma a Najeriya.

Ta ce Gwamnatin Tarayya za ta mallaki hekta 100,000 ta gona duk jiha a Najeriya domin noma kayan abinci tare da gina hanyoyi a wannan wurare don samar wa manoma damar kai amfanin gona zuwa kasuwanni da rage asarar ta ke biyo bayan girbi.

A wata zanta wa da Ministan Noma na Najeriya, Alhaji Sabo Nanono ya yi da BBC, ya ce za a karbo bashin ne domin zamanantar da aikin noma tare da inganta shi a kananan hukumomi 632 na kasar.

Minista Nanono ya ce za a yi amfani da wannan kudi wajen sayo motocin noma da kayan gyaransu da gina wuraren ajiye kayan feshi da magungunan kwari da sauransu.