Gwamnati ta raba wa mata masu karamin karfi 15 injin niƙa a Edo

Ma’aikatar noma ce ta raba tallafi kyauta

Gwamnati ta raba wa mata masu karamin karfi 15 injin niƙa a Edo

Nasiru isiyaka yana kokarin tayar da injin nika.

Gwamnatin Tarayya ta raba wa wasu mata masu karamin karfi su 15 tallafin injin niƙa a Jihar Edo.

Ma’aikatar Ayyukan Gona da Samar da Abinci ta kasa ce ta raba kayan a wani mataki na wadata kasa da abinci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) an ba kowacce daga cikin mata 15 din kyautar injin nika guda daya.

Babban Jami’i a ma’aikatar, Peter Pindar, ya ce an raba kayan ne karkashin shirin samar da tallafi ga mata da matasa kan hanyoyin sarrafa doya da adana ta domin ci gaban kasa.

A cewar Peter, ma’aikatar ta sayo injinan ne domin raba su ga mata a wani mataki na karfafa musu gwiwa. (NAN)

’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe