Gwamnati ta rage kudin jarabawar UTME, SSCE, JSCE
Gwamnatin Tarrayyar Najeriya ta amince a rage kudin fom din jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan, JAMB UTME da jarrabawar kammala makarantun sakandare National Examination Council (NECO) SSCE, da jarrabawa (JSCE). Daga yanzu duk dalibin da zai rubuta jarrabawar kammala sakandare, NECO, zai sayi fom din ne a kan Naira 9,850 maimakon Naira 11,350 da […]
Gwamnatin Tarrayyar Najeriya ta amince a rage kudin fom din jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan, JAMB UTME da jarrabawar kammala makarantun sakandare National Examination Council (NECO) SSCE, da jarrabawa (JSCE).
Daga yanzu duk dalibin da zai rubuta jarrabawar kammala sakandare, NECO, zai sayi fom din ne a kan Naira 9,850 maimakon Naira 11,350 da aka saba saya.
An kuma rage kudin fom din jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare JAMB daga Naira 5,000 zuwa Naira 3,500.
Hakan zai fara aiki ne daga watan Janairun 2019.