Gwamnati ta rufe gidan marayu da aka sace yara 26 a Kogi

Daga bisani sojoji suka kuɓutar da sauran mutum tara a ranar Alhamis 7 ga watan Mayu tare da haɗa su da iyalansu

Gwamnati ta rufe gidan marayu da aka sace yara 26 a Kogi

Kujeru a cikin aji a makarantar Bethel Baptist a Damishi, Jihar Kaduna inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai fiye da 100. (Hoto: Reuters). 

Gwamnatin Kogi ta rufe makarantar Daarul Kitab Islamin da ke yankin Zariagi a Ƙaramar Hukumar Adavi, bisa zargin fara aiki ba tare da amincewar gwamnatin jihar ba.

A ranar 26 ga watan Afrilu, 2026 ne wasu ’yan bindiga suka kai hari makarantar marayun inda suka sace ɗalibai 26 har da matar mamallakin makarantar.

Jami’an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da mutum 17 daga cikin waɗanda aka sace jim kadan bayan faruwar lamarin.

Daga bisani sojoji suka kuɓutar da sauran mutum tara a ranar Alhamis 7 ga watan Mayu tare da haɗa su da iyalansu.

Sai dai Kwamishinan Ilimi na jihar, Wemi Jones, ya jagoranci wani ayari daga Ma’aikatar Ilimi ta jihar zuwa makarantar a ranar Alhamis inda suka rufe ta, tare da umartar mamallakinta da ya gaggauta bayyana a gaban ma’aikatar.

Kwamishinan ya bayyana cewa makarantar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai gwamnati ta gamsu cewa an cika duk sharuɗɗan da ake buƙata wajen kafa makaranta kafin a sake buɗe ta domin gudanar da harkokin karatu.

Ya ce gwamnatin jihar na sane da nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da cewa makarantu a faɗin jihar suna da inganci, tare da kasancewa cikin yanayi mai kyau da tsaro domin koyarwa da koyo.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi sassauci wajen tabbatar da ƙa’idojin kafa makarantu ba, yana mai jaddada cewa alhakin gwamnati ne tabbatar da makarantu sun kasance masu inganci da tsaro.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa duk da yunƙurin da mamallakin makarantar ya yi na fara rajistar makarantar, bai kamata a buɗe ta ba kafin samun cikakkiyar amincewar gwamnati.