Gwamnati ta rufe makarantu bayan cutar Diphtheria ta kashe dalibai 5 a Bauchi
Gwamnatin ta ce duk makarantar da aka samu cutar a nan gaba, za a rufe ta

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed. (Hoto: Ttwitter.com/SenBalaMohammed)
Dalibai biyar sun mutu sanadiyyar wata cuta da ake zargin ta Diphtheria a Karamar Hukumar Jama’are da ke Jihar Bauchi.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dokta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi ranar Laraba.
- ’Yan sanda na neman masu tunzura Ale Rufai Mai Gangaliyon
- ECOWAS ba za ta lamunci juyin mulki a Nijar ba —Tinubu
Ya kuma ce an dauki samfurin mutum 28 a Karamar Hukumar, inda biyu daga ciki aka tabbatar da sun kamu da ita, inda ya ce za su tashi tsaye wajen dakile yaduwarta.
Shugaban ya bayyana bullar cutar a matsayin abin damuwa, kuma yanzu haka za a ci gaba da bincike domin tabbatar da ko cutar ce ta kashe su.
Ya kuma ce za a bayar da allurar rigakafi domin kare ci gaba da yaduwarta.
“Za mu fara yi wa yaranmu rigakafin tun suna mako shida a duniya, kuma babban abin dadin shi ne allurar kyauta ce.
Dokta Rilwanu ya kuma ce tuni gwamnati ta rufe dukkan makarantun da aka samu rahoton bullar cutar a yankin domin takaita ci gaba da yaduwarta.
Ya kuma ce duk makarantar da aka samu rahoton bullar cutar a Jihar, za a rufe ta.