Gwamnati ta ruguza kasuwar kayan lantarki ta Oshodi
A ranar Larabar da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Legas ta ruguza kasuwar kayan lantarki ta Oshodi, mai dadadden tarihi, kasuwar da ta shafe sama da shekaru 40 ana hada-hada a cikinta.An gudanar da ruguza kasuwar ce da misalin karfe takwas saura kwata na safiyar Larabar da ta gabata, a yayin da gwamnan jihar, Akinwunmu […]
A ranar Larabar da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Legas ta ruguza kasuwar kayan lantarki ta Oshodi, mai dadadden tarihi, kasuwar da ta shafe sama da shekaru 40 ana hada-hada a cikinta.
An gudanar da ruguza kasuwar ce da misalin karfe takwas saura kwata na safiyar Larabar da ta gabata, a yayin da gwamnan jihar, Akinwunmu Ambode da kansa ya jagoranci manyan mukarraban gwamnatinsa, wadanda suka hada da Kwamishinan Al’amuran Muhalli, Dokta Babatunde Adejere da jami’an ’yan sanda, aka gudanar da aikin, wanda aka tafiyar da shi ba tare da wata tirjiya daga mamallakan shagunan kasuwar ba.
Tun da farko, a ranar Litinin da ta gabata ce jami’an yaki da rashin da’a da aka fi sani da KAI tare da rakiyar jami’an ’yan sanda suka kulle kasuwar, tare da cewa tana haddasa kunci ga al’umma.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Legas, Mista Stebe Ayorinde ya ce, an dauki matakin ruguza kasuwar ne domin a tsaftace yankin Oshodi da kuma sake wa unguwar Owonifari fasali zuwa wanda ya dace.
“Muna shirin canza wa Unguwar Owonifari fasali, yadda za ta dace da zamani, za a gina sabuwar tashar mota wadda ta dace, yadda motoci za su samu wurin ajiya wanda ya dace. Inji shi.
Ya kuma kara da cewa, dukkan ’yan kasuwar da suke da shaguna a kasuwar da aka ruguza, an mayar da su sabuwar kasuwar Isopakodowo da ke Bolade.