‘Gwamnati ta sa hannu don inganta magungunan gargajiya’
Aminiya ta tattauna da wani matashin wanzami mai suna Dokta Salisu Wanzami wanda ke harkar magungunan gargajiya kan gudunmawar da sana’arsu take bayarwa wajen kiwon lafiya: Shin wannan sana’a ta wanzanci gadarta ka yi ko a sama ka shige ta? A gaskiya gadarta na yi don na tashi na ga kakana shi ne Sarkin […]
Aminiya ta tattauna da wani matashin wanzami mai suna Dokta Salisu Wanzami wanda ke harkar magungunan gargajiya kan gudunmawar da sana’arsu take bayarwa wajen kiwon lafiya:
Shin wannan sana’a ta wanzanci gadarta ka yi ko a sama ka shige ta?
A gaskiya gadarta na yi don na tashi na ga kakana shi ne Sarkin Askar Garin Mani a Jihar Katsina, sannan mahaifina na tashi na ga yana bayar da taimako irin na maganin gargajiya to haka dai na yi kokari na gada kamar yadda na ga ni wajen iyaye da kakannina.
Kuna da wata hadaka da gwamnati ne kan yadda za ta rika ba ku horo ko kuna da wata makaranta ce ta samun horo?
To in dai na samu horo ne a gida domin kamar yadda na fada a baya iyaye da kakannina ne suka horar da ni. Na tashi na ga suna wannan sana’a sai suka koya min. Amma maganar gwamnati ko wasu kungiyoyi su horar da ni ban samu wannan ba. Iyaye da kakanninmu sun shiga da ni daji suka nuna mana wancan in an hada shi da wannan zai yi maganin abu kaza, sai muka san yadda za mu yi mu hada kuma muka hada mu ke bai wa jama’a kuma suna samun biyan bukata. Amma idan misali gwamnati ta bukace mu kuma ta tantance mu ta wajen hada magunguna to a shirye muke mu bayar da hadin kai.
Yaya dangankatakarku da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), wajen lura da ingancin sana’ar taku?
Wannan hukuma tana da kokari wajen tantance magunguna, ni ma na kusa cika duk wasu sharudda da ta gindaya na mu cika kafin ta yi mana rajista ta ba mu lamba.Tana kokarin sanin yaya nake samo wannan magani? Yaya nake hada shi, kuma yaya ake shanya shi ko ake tsabtace shi? Sannan wane tabbaci kake da shi cewa zai yi maganin abu kaza? Duk sai ta bincike ka ta tantance, ta ji sahihancin yadda kake yin komai, ta tabbatar wannan maganin yana aiki kuma ba zai cutar da al’umma ba, sannan ta yarda ta karbe ka ta ba ka lambar amincewa.
Akasari yanzu za ka ga masu tallar magungunan gargargajiya ko’ina, wane kokari kuke yi don ganin an tsabtace wannan sana’a taku?
To e wannan gaskiya ce, ina tabbatar maka cewa a yanzu mun dauki matakai da dama, musamman a nan Jihar Borno muna kokarin gudanar da tarurruka a kowane karshen mako saboda mu kawar da batagari da ke shigowa suna bayar da magungunan da ba su dace ba, wadanda ke cutar al’umma domin neman kudi. Muna da wani kwamiti na masu duba wannan matsala, sannan akwai ’yan sandan magani da suke fita sintiri suna farautar irin wadancan batagari a kasuwanni da kowane lungu da sako su kamo su mu kuma mu dauki matakin hukunta su.
Shin kun taba tuntubar gwamnati ta fuskar tallafa muku ku fito da wani tsari kan yadda za ku rika sarrafa magungunan gargajiya su koma tamkar na Bature?
A kwanaki mun kai wa gwamnati kuka cewa muna bukatar wajen da za a ce yau a Jihar Borno muna da kasuwar da ake sayar da magunguna kawai wato kasuwar magani. A ce muna sarrafa shi kamar yadda ake yi a wasu kasashen duniya, wanda hakan zai taimaka wajen ingancin maganin. A yanzu dai muna fata Gwamna Babagana Umara Zulum, zai taimaka wajen inganta harkar magungunan gargajiya.
Shin kamar yara nawa kake da su?
A yanzu haka ina da yara da dama, wadansu magidanta da iyali, suna zuwa su karbi kayan sana’a su fita su je su yi sana’a su dawo in sallame su, yayin da wadansu ’yan makaranta ne suna zuwa karatun boko, idan an taso daga makaranta su zo su dauki kayan sana’a don su samu abin da za su biya kudin makaranta. Sannan wadansu kuma almajirai ne in sun tashi daga karatu maimakon su je bara sai su zo su dauki kayan sana’a su fita su samo abin da suka samu in sallame su su koma wajen karatunsu. Ina da yara da yawa wadansu na yaye su, wadansu yanzu haka suna Kano wadansu Kaduna, wadansu kuma suna kudancin kasar nan, a yanzu ina da yara sama 50, wadanda suke ci a karkashina.
A karshe wane kira kake da shi ga ’yan uwanka masu maganin gargajiya don inganta sana’arku, sannan wane kira kake da shi ga gwamnati?
Ina kira ga ’yan uwana masu maganin gargajiya cewa su ji tsoron Allah. Mu tsaya mu yi gaskiya tsakaninmu da Allah, kuma ka tabbatar ka dauki maganin da mutum ya nema ka ba shi kada ka ba shi maganin da ba shi ne cutar da take damunsa ba. Kada ka dauki maganin wani abu daban ka bayar ga mutum a matsayin maganin wani abu daban ya sha bai masa amfanin komai ba.
Ga gwamanati kuma wannan Gwamna na Borno mai adalci ne, don mun fahimci cewa yana da burin ya taimaka wa al’ummarsa don su ci gaba ta kowace fuska. Saboda da zarar wani abu ya faru to yanzu za ka ga ya je wajen. Muna fata Allah Ya yi masa jagora, kuma muna fata ya taimaka wajen bunkasar ci gaba harkar magungunan gargajiya a jiharsa.