Gwamnati ta sake tunani kan daina sayar da Dala ga masu shigo da kayan abinci
Shugaban Kungiyar Masu Shayi ta Najeriya, Alhaji Shu’aibu Abubakar, ya yi kira ga gwamnati ta sake tunani, kan sanarwar da ta bayar na daina sayar da Dala ga masu shigo da kayan abinci daga waje da Babban Bankin Najeriya (CBN), yake yi. Alhaji Shu’aibu Abubakar ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da […]
Shugaban Kungiyar Masu Shayi ta Najeriya, Alhaji Shu’aibu Abubakar, ya yi kira ga gwamnati ta sake tunani, kan sanarwar da ta bayar na daina sayar da Dala ga masu shigo da kayan abinci daga waje da Babban Bankin Najeriya (CBN), yake yi.
Alhaji Shu’aibu Abubakar ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos, inda ya ce “Muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta sauya tunani kan umarnin da ta bayar na kada Bankin CBN ya sayar da Dala ga wadanda suke shigo da kayan abinci daga waje.”
Ya ce idan wannan umarni ya fara aiki, farashin kayayyakin masarufi zai yi tashin gwauron zabo. Kuma idan farashin kayayyakin masarufi ya kara tashi, talakawa za su dada shiga mawuyacin hali a kasar nan. Ya ce “Don haka muna kira ga Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai su zauna su sake duba wannan al’amari, domin guje wa sake dada jefa talakawan Najeriya A cikin mawuyacin hali.”