Gwamnati ta sauke wajibin da ke kanta kafin ta kara haraji – Dillalan motoci

Alhaji Kabiru Sa’idu shi ne Manajan Daraktan Kamfanin Sayar da Motoci na Katsinawa da ke Bauchi, kuma Shugaban Kungiyar Dillalan Motoci ta Jihar Bauchi a zantawar da ya yi da Aminiya ya bayyana ire-iren matsalolin da kungiyarsu ke fuskanta da yadda gwamnati za ta warware su, inda ya ce sai gwamnati ta samar da tsaro […]

Gwamnati ta sauke wajibin da ke kanta kafin ta kara haraji – Dillalan motoci

Alhaji Kabiru Sa’idu, Shugaban Kungiyar Dilllalan Motoci ta Jihar Bauchi

Alhaji Kabiru Sa’idu shi ne Manajan Daraktan Kamfanin Sayar da Motoci na Katsinawa da ke Bauchi, kuma Shugaban Kungiyar Dillalan Motoci ta Jihar Bauchi a zantawar da ya yi da Aminiya ya bayyana ire-iren matsalolin da kungiyarsu ke fuskanta da yadda gwamnati za ta warware su, inda ya ce sai gwamnati ta samar da tsaro da wutar lantarki da sauransua masu biyan harajin su samu kudin biya kafin ta kara haraji:

Kwanakin baya Hukumar Kwastam ta rufe wuraren da ake sayar da motoci yaya kuka ga wannan mataki kuma wani mataki za ku dauka?

Abin da yake gudana ya yi mana ba-zata, domin abu ne da ya zama sabo, don ba mu da masaniyar hakan zai faru a matsayinmu na abokan huldarsu. Mun sa ran duk abin da zai faru za su neme mu su sanar da mu, amma kawai sai muka wayi gari muka tarar suna rufe gidajen mota a wasu jihohi.

Akwai gidajen mota da aka rufe aka hana su gudanar da huldodinsu kuma sun bi gidajen motoci suna tambayar takardun motocin da ake da su ko an biya musu harajin shigowa mai kyau, ko ba a biya ba. Abin da ya faru din ya yi matukar daga mana hankali kuma ya ba mu mamaki a matsayinmu na ’yan kasa masu biyayya ga dokar kasa. Muna ganin da duk abin da gwamnati za ta yi za a ba mu ’yancinmu na ’yan kasa, wajen rashin kawo mana barazana da tashin hankali cikin harkokin kasuwancinmu.

Kun daidaita ne da su ne?

Gwamnati ka san ita take da tsari ba ka da zabi sai abin da ta ce, kuma an fada mana cewa tana zargin masu sayar da motoci a Najeriya suna shigo da motoci da yawa wadanda ba a biya musu kudin haraji, amma abin da ta ja hankali a kai shi ne ta ba da dama duk wanda yake da mota a Najeriya ya biya kudin haraji a ofishin Hukumar Kwastam.

Sai dai abin da muke so mu ja hankalin gwamnati a kai shi ne ta duba da idon basira halin da mutane suke ciki na matsi, kuma akwai tsari da aka ce an fitar na a biya kashi 35 cikin 100 na harajin akwai kuma wasu tsarabe-tsarabe da su ma suka kai kashi bakwai, wanda idan ka tara sun kai kashi 42 cikin 100 na kudin motar da kake da ita. Gwamnati ta duba wannan tsari wajen rage wa mutane wannan kudi.

A nan Bauchi ba a rufe muku gidajen motocinku ba ko akwai fargabar za su iya rufewa?

Dama ce da aka bayar cewa duk motar da ba a biya mata kudin haraji ba, sai an biya ko tana gidan sayar da mota ko wacce aka ajiye a wani waje, kuma mun kira zama mun tattauna a kan wannan matsala mun ba su shawara duk wanda ya san yana da motar da ba a biya mata haraji ba ya je ya biya, domin ya yi kasuwancinsa cikin kwanciyar hankali, kuma muna ba wa gwamnati shawara idan tana neman kudi ta yi hakuri kada ta razana ’yan kasa.

Kullum muna fada cewa kudi bai kai kimar dan Adam ba, gwamnati ya kamata ta duba barazanar da ake samu na daga hankalin mutane ko duk wani abu da zai kawo hayaniya kada ta sake goyon bayan haka.

Ko sun kama wasu daga cikin mutanenku?

A nan dai ba ko mutum daya da aka kama, kuma tsirarun wurare ne aka samu motocin da aka kama wadanda ake zargin ba su da takarda, kuma ana bin diddigi takardun da masu motar suka bayar ya zama an biya musu kudin da ake tunanin ba a biya musu ba, kuma muna da yakinin an biya da izinin Allah.

Mene ne babban kalubalen da kuke fuskanta a matsayinku na dillalan motoci?

Kalubalen wannan sana’a tamu yana da yawa, amma wanda yake ci mana tuwo a kwarya shi ne hatsaniya a tsakaninmu da Hukumar Kwastam, wanda kuma mu abokan juna ne, idan su jami’an gwamnati ne masu nema mata kudi, mu kuma mu ne ’yan kasuwar da za mu samo kudin mu ba gwamnati. Ya kamata a ce akwai alaka mai kyau tsakaninmu dasu, idan abin da ake ganin muna yi ba daidai ba ne sai a kira mu mu gyara, ita gwamnati dukkan harkokin da ya kamata ta saurare mu ta ji kokenmu abin da ya kamata a tausaya mana a kuma sassauta mana domin mu zama masu bin doka da oda.

Wadansu na cewa kasuwanci a Najeriya ana yin sa cikin tashin hankali sakamakon kare-karen kudin haraji da barazana ko ku ’yan kasuwa kuna ganin haka?

Eh, lallai haka ne kwanakin baya na yi hira da ’yan jarida a kan maganar karin haraji da  gwamnati take so ta tashi daga kudin da take samu daga man fetur, yana da kyau idan kasa akwai ci gaba akwai masana’antu akwai wutar lantarki akwai tsaro yadda duk wanda ka ce ya zo ya zuba hannun jari a kasa zai zuba domin ’yan kasa su samu aikin yi.

Ya zama ba masu zaman banza da yawa kowa na da aikin da idan an ce za a karbi haraji a hannunsa zai iya bayarwa. Amma muddin gwamnati ba ta yi kokarin inganta tsaro da wutar lantarki da duk abin da ya kamata na hakki da ke kanta domin masu zuba jari daga waje su zo, su zuba ’yan kasa kowa ya samu abin yi to ba  za a samu harajin da ake nema ba.

Akwai maganar da gwamnati ta yi cewa za a rika amfani da kudin China da na Najeriya ku ’yan kasuwa yaya kuke kallon wannan lamari?

Gaskiya abin farin ciki ne musamman  ’yan kasuwarmu da suke zuwa kasar China saye da sayarwa. Wannan babban ci gaba ne domin a da sai ka yi canjin Dala ko Yuro yanzu kuma ka samu kai-tsaye, watakila ya zama ko daga Najeriya ya zama Babban Bankin Najeriya (CBN) yake da hada ka da kasar China kai kawai abin da za ka yi shi ne kazabi kayan da kake so a yi maka, sannan ka biya kudinka a CBN shi kuma ya san yadda zai yi ta biya kasar China kudin.

Lallai wannan abu ne mai kyau kuma ’yan kasuwa suna marhabin da zuwansa ina fata gwamnati za ta ba da himma wajen ganin abin da ta dauko domin ganin ya tabbata an yi shi cikin kankanen lokaci ’yan kasa su amfana.

Wani sako kake dashi?

Sakon da nake da shi zuwa ga hukuma shi ne lallai muna wa shugabanninmu fatar alheri kuma Ubangiji Ya shiga cikin lamarinsu kada Ya bar su da iyawarsu Ya taimaka musu Ya sanya musu basira da sauraron dukkan al’ummar da suke ba su shawarwari, na kusa da na nesa. Duk wanda ya zo da magana a dauka a sa a ma’auni a dauki masu amfani a ciki don ganin cewa mun gudu tare mun tsira tare mun kai wannan kasa tamu ga tudun-mun-tsira.