Gwamnati ta sauya gurbin shugaban TetFund

A yau Litinin ne aka sanar da korar shugaban Gidauniyar kula da manyan makarantun Najeriya wato Tetfund Dakta Abdullahi Bichi Baffa daga mukaminsa. Yayin da ma’aikan Tetfund suka yi matukar  mamakin irin wannan sanarwar, bayan sauke Baffah an maye gurbinsa da Suleiman Bogoro wanda jagoranci gidauniyar a baya. Bogoro dai ya kama aiki a yau […]

Gwamnati ta sauya gurbin shugaban TetFund

A yau Litinin ne aka sanar da korar shugaban Gidauniyar kula da manyan makarantun Najeriya wato Tetfund Dakta Abdullahi Bichi Baffa daga mukaminsa.

Yayin da ma’aikan Tetfund suka yi matukar  mamakin irin wannan sanarwar, bayan sauke Baffah an maye gurbinsa da Suleiman Bogoro wanda jagoranci gidauniyar a baya.

Bogoro dai ya kama aiki a yau tare da takardar fara aikin ofishinsa.

Ma’aikatar ilimi ce ta sanar da sauyin kamar yadda Mataimakin Daraktan sadarwa Bem Goong ya sanar.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta