Gwamnati ta sayo na’urorin sauraren hirar mutane ta wayar salula
Gwamnatin Shugaba kasa Goodluck Jonathan ta sayo injinan da za su rika sauraren maganganun da mutane suke yi ta wayar salula domin gano irin maganganun da mutane suke tattaunawa a sirrinsu. Wadannan na’urori dai an kashe Naira biliyan 11 wajen sayo su kuma Rundunar ’Yan sanda ta kasa da Hukumar Leken Asiri ta kasa da […]
Gwamnatin Shugaba kasa Goodluck Jonathan ta sayo injinan da za su rika sauraren maganganun da mutane suke yi ta wayar salula domin gano irin maganganun da mutane suke tattaunawa a sirrinsu.
Wadannan na’urori dai an kashe Naira biliyan 11 wajen sayo su kuma Rundunar ’Yan sanda ta kasa da Hukumar Leken Asiri ta kasa da Hukumar Sadarwa da ta Kimiyyar Sararin Samaniya (NIGCOMSAT) ne za su kula da gudanar da irin wannan bincike.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta yi bincike a kai ta ce, tuni har an kakkafa na’urorin kuma an fara aiki da su.
Jaridar ta ce duk da wadannan kudi ba sa cikin kasafin kucin kasa, Shugaba Jonathan ya yi gaban kansa ne ba tare da amincewar majalisar tarayya ba ya debi wadannan makudan kudi domin sayo wadannan na’urori.
Bin diddigi da zuko maganganun mutane haka kawai ba tare da wani dalili ko na tsaro ba, ya saba wa dokar kasa, inji jaridar.