Gwamnati ta taimaka wajen kashe harkar auduga a kasar nan – A. A. Master

Tsohon Shugaban Cibiyar Kasuwanci ta Jihar Zamfara Alhaji A. A. Masta ya zargi Gwamnatin Tarayya da kashe harkar auduga a kasar nan. Alhaji A. A. Master ya bayyan haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gusau, inda ya ce gwamnatin ta kashe harkar auduga ce ta hanyar rashin ba manomanta da masu kasuwancinta […]

Gwamnati ta taimaka wajen kashe harkar auduga a kasar nan – A. A. Master
Gwamnati ta taimaka wajen kashe harkar auduga a kasar nan – A. A. Master

Tsohon Shugaban Cibiyar Kasuwanci ta Jihar Zamfara Alhaji A. A. Masta ya zargi Gwamnatin Tarayya da kashe harkar auduga a kasar nan. Alhaji A. A. Master ya bayyan haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gusau, inda ya ce gwamnatin ta kashe harkar auduga ce ta hanyar rashin ba manomanta da masu kasuwancinta tallafi ko bashi da bai da ruwa. Ya ce masaku da kwamfanonin gurza auduga duk sun mutu saboda rashin tallafi da kula kuma wannan ya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali, yayin da wasu ’yan kasuwar auduga da suka koma sayan waken suya ko ridi. Ya ce Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi noman auduga a kaswar nan, don haka ya bukaci gwamnati ta sake tunani ta samar wa manoma da ’yan kasuwar auduga tallafi ko bashi marar ruwa, don ci gaba da bunkasa harkar auduga a kasar nan. Ya koka kan yadda jama’ar kasar ke kin sayen atamfofinmu suna sayen na kasasshen waje, inda ya shawarci gwamnati ta fito da tsari na musamman da zai taimaka wajen hana shigo da atamfa daga waje domin kare masakun kasar nan.

 

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi