Gwamnati ta tsame hannunta a harkar sufurin jiragen sama – Kyaftin AbdulSalam
Shugaban Kwalejin fasahar tukin jiragen sama ta Najeriya (NNCAT) Zariya Kyaftin AbdulSalam Mohammed ya ce a shekarar 1977 kwalejinsa ta horar da dalibai 88, amma a halin yanzu ana yaye kwararrun matuka jirgin sama da 300, baya ga bunkasar kwaleji, wadda ya ce ita ce mafi saukin kudin karatu in an kwatanta da takwararta da […]

Shugaban Kwalejin fasahar tukin jiragen sama ta Najeriya (NNCAT) Zariya Kyaftin AbdulSalam Mohammed ya ce a shekarar 1977 kwalejinsa ta horar da dalibai 88, amma a halin yanzu ana yaye kwararrun matuka jirgin sama da 300, baya ga bunkasar kwaleji, wadda ya ce ita ce mafi saukin kudin karatu in an kwatanta da takwararta da ke Ilorin, ya kuma yi karin haske kan matsalolin da suka dabaibaye jiragen kasa, musamman Nigeria Airways, wadda ya ce katsalandan ya kassara shi.
A hirarsa da editocin jaridar Dailytrust da Aminiya, Kyaftrin AbdulSalam Mohammed, ya ce duk da tarin matsalolin da kwalejhin ke fama da su, a halin yanzy suna shirin samar da na’urar horar da matukan jirgin sama ta B737 Nedt Gen flight simulator ta zamani. “Da zarar an kafa na’urar babu sauran cewa kamfanonin jiragen sama da ke amfani da jirgi samfurin Boeing su rika tura matukansu wasu kasashe don smaun horo. Yin hakan zai taimaka wajen adana yawan ku8din musayar waje da ake kashewa. Kuma muna shirin bullo da bayar da horon tuka karamin jirgin helicopter. Kodayake dama muna horar da matuka kananan jirage tsawon kafuwar kwaleji shekara 53. Yin hakan ya zama dole saboda bukatarsa da ake yi a kamfanonin hada-hadar hakar man fetur da iskar gas,” inji shi.
Kyaftin AbdulSalam ya bayyana yadda za su shawo kan rashin aikin yi ga matukan da suka samu horon tukin jiragen sama a kasar nan. “daukacin wadanda suka karanci aikin jirgin sama, musamman sashen bayar da umarnin sauka da tashi duk hukumar kula da filayen jiragen kan dauke su aiki, amma ban da matukan. Don haka muke son bullo musu da tsarin da zai ba su damar cin dogon zango da yawan sa’o’i da ake bukata ga kowane matuki ya karade, ta yadda zai rika samun ci gaba a aikinsa,” kamar yadda ya bayyana.
Da yake tsokaci kan yadda za a bunkasa harkokin yawon bude ido da saka jari a kasar nan, ya bayyana cewa sai gwamnati ta tsame hannunta daga hada-hadar sufurin jiragen sama sannan za a samu ci gaba, domin a cewarsa kasar Habasha da ta yi shuhura a harkar sufurin jiragen sama kwararru ta bai wa suke kula da harkar duk da cewa gwamnatin kasar na da hannu a ciki. Sai mu a nan Najeriya lokacin da ake da jirgin Nigerian Airways wasu manyan kasa ko jami’an gwamnati kan yi katsalandan a harkar, ta yardar tun ana samun riba har ta durkushe.
A cewarsa: “An taba tafiya Landan da jirgin Nigeria Airways, amma bai fi kashi 20 cikin 100 na fasinjopjin suka biya kudin tikitin su ba. Irin wadannan al’amura da za a hana su, sai kawai gwamnati ta rike kasha biyar cikin 100, sannan a mika ragamar gudanar da harkar a hannun kwararru. To tabbas za mu kai ga gaci kamar yadda kamfanonin sufurin jiragen sama nja Ethiopia Air da emirates suka shahara a wannan duniya.”
Shugaban kwalejin ya karkare batutuwansa tare bayar da tabbacin cewa shirin kafa jirgin yana nan a kasafin kudin bana. “A matsayina na shugaban kwamitin da Gwamnati ta dora wa alhakin tsara yadda za a samar da jirgin sama mallakar kasar nan, mun bayar da shawarwasrin nda suka dace. Kuma a halin yanzu ina mai tabbatar muku cewa a yi wa shirin tanadi a cikin kasafin kudin 2017, wato banan nan ke nan.” Inji shi.