Gwamnati ta yi ƙarin haske kan fargabar rasa ayyuka yayin aiwatar da Rahoton Oronsaye

’Yan Najeriya sun fara ganin alfanun sauye-sauyen da Tinubu ke jagoranta a sassa daban-daban.

Gwamnati ta yi ƙarin haske kan fargabar rasa ayyuka yayin aiwatar da Rahoton Oronsaye

Gwamnatin Tarayya ta kwantar da hankalin ma’aikata dangane da Rahoton Oronsaye da ta ba da izinin aiwatarwa.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin da ta gabata ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da Rahoton Stephen Oransaye na shekarar 2012, wanda ya bai wa Gwamnatin Goodluck Jonathan shawarar haɗe wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda ayyukan su ke da alaƙa, a wani mataki na rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

Wannan sanarwar dai ta jefa kokwanto a zukatan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ke fargabar wasunsu ka iya rasa ayyukansu a dalilin aiwatar da Rahoton Oronsaye.

Sai dai a sanarwar da Gwamnatin Tarayyar ta fitar, ta ce babu ma’aikacin da zai rasa aikinsa wajen aiwatar da rahoton Oronsaye, wanda ke neman a haɗe ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

Ministan Labarai da Wayar da kan Jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba a taron manema labarai karo na hudu na ministoci.

“Abin nufi shi ne gwamnati na son rage tsadar kayayyaki da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyuka.

“Ba wai yana nufin gwamnati na shirin korar ma’aikata ko jefa mutane cikin kasuwar kwadago ba,” inji shi.

Ministan ya ce aiki da rahoton wata alama ce karara ta jajircewar Shugaba Tinubu na yin taka-tsantsan a kasafin kudi da gudanar da mulki ta hanyar yin nazari mai zurfi a kan kwamitocin gwamnati, da hukumomi, da ma’aikatun gwamnati.

Ya ce amincewa da yin aiki da rahoton na Orosanye, wanda ya biyo bayan nazari mai zurfi, shi ne tabbatar da cewa ba a yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyuka masu muhimmanci, sannan kuma a magance bukatun ‘yan kasa yadda ya kamata tare da sanya bukatun al’umma a gaba.

“Ta hanyar aiwatar da rahoton Oronsaye, Shugaba Tinubu yana da niyyar cimma babban tanadin farashi ta hanyar kawar da maimaita ayyuka da daidaita tsarin gudanarwa, da inganta rabon albarkatu.”

“Wannan tsari na sa ido zai bai wa gwamnati damar gudanar da aiki yadda ya kamata tare da kiyaye inganci da isar da ayyuka ga al’ummar Najeriya,” inji shi.

Ministan wanda ya ce ‘yan Najeriya sun fara ganin alfanun sauye-sauyen da shugaban ƙasa ke jagoranta a sassa daban-daban, ya jaddada cewa rahoton da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar na nuni da cewa Najeriya ta samu ƙaruwar kuɗin da ake samu a cikin ƙasa da kashi 3.46 cikin 100.