Gwamnati ta yi Allah wadai da kisan mutum 9 a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kakkausar suka tare da yin Allah wadai da harin da wadansu mahara da ba a san ko su wane ne ba suka kai a kauyen Nandu da ke Karamar Hukumar Sanga a kudancin jihar da ya yi kaurin suna wajen kai hare-haren da ke da nasaba da daukar fansa. Kakakin […]

Gwamnati ta yi Allah wadai da kisan mutum 9 a Kaduna

Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kakkausar suka tare da yin Allah wadai da harin da wadansu mahara da ba a san ko su wane ne ba suka kai a kauyen Nandu da ke Karamar Hukumar Sanga a kudancin jihar da ya yi kaurin suna wajen kai hare-haren da ke da nasaba da daukar fansa.

Kakakin Gwamnan Nasir El-Rufa’i na Jihar, Mista Samuel Aruwan Aruwan, wanda ya tabbatar da rasuwar mutum tara tare da kona gidaje a harin da aka kai ranar Jumu’ar da ta gabata da dare, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, ciki har da kananan yara, inda ya ce tuni gwamnatin jihar ta tura jami’an tsaro yankin.

“Babu abin da rikici ke haifarwa face salwantar da rayuka da jikkata wadansu tare da kone-konen dukiyoyi da gidaje da jefa tsoro da razana a zukatan mutane. Lokaci ya yi da ya kamata mu rika girmama junanmu a matsayinmu na mutane ta hanyar magance sabanin da ke tsakaninmu cikin lumana tare da kai rahoton duk wani abu da aka gani, wanda zai iya haifar da tashin hankali,” inji sanarwar.

Takardar ta yi kira ga jami’an tsaro da shugabannin addini da sarakunan gargajiya su hada kansu wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a cikin al’umma.

Shugaban Karamar Hukumar, Mista Charles Danladi ya tara matasan yankin inda ya gargade su kan su guji duk wani abu da ka iya ruruta rikicin zuwa wasu sassa da sunan daukar fansa.

Wani daga cikin mutanen garin da rikicin ya shafa, wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa yana ganin harin ba ya rasa nasaba da daukar fansar da makiyaya suka yi sakamakon wani hari da aka kai musu gab da zabubbukan da suka gabata, inda aka kashe shanu 11 da tumaki 28.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta kai dauki da kayayyakin tallafi a yankin da abin ya shafa.