Gwamnati ta yi daidai – Talakawa

Aminiya ta nemi jin tab akin talakawa game da wannan matakin da gwamnatin Kaduna ta dauka. Inda Salisu Suleiman ya bayyana cewa bai dace ba gwamnati ta rika daukar nauyin malamai ko ‘yan siyasa zuwa aikin hajji ko Jerusalem’. ‘’ Ina ganin wannan kudin da ake kashewa wajen daukar nauyin irin wadannan mutanen kamata ya […]

Gwamnati ta yi daidai – Talakawa
Gwamnati ta yi daidai – Talakawa

Aminiya ta nemi jin tab akin talakawa game da wannan matakin da gwamnatin Kaduna ta dauka. Inda Salisu Suleiman ya bayyana cewa bai dace ba gwamnati ta rika daukar nauyin malamai ko ‘yan siyasa zuwa aikin hajji ko Jerusalem’. ‘’ Ina ganin wannan kudin da ake kashewa wajen daukar nauyin irin wadannan mutanen kamata ya yi gwamnati ta yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan da za su taimaka wa talakawa. Duk da cewa su ma wadanda ake kaiwa suna da hakki a gwamnati, amma ya fi dacewa a yi aiki da kudin domin kowa ya amfana ba,dan wasu mutane ‘yan kalilan ba.
Shi ma Ibrahim Mairago, mataimakin Sakataren jam’iyar APC a gundumar Sabon Gari, cewa ya yi gwamnati ta yi daidai, domin  dama ba kananan ‘yan Siyasa ake bai wa kujerun hajjin ba. Manyan idan sun samu kujerun daga su ne sai iyalansu. Haka kuma wadansu malaman idan an ba su kujerun su ma iyalansu kawai suke tunawa, wannan ya sa nake goyan bayan matakin da gwamna ya dauka.