Gwamnati Tarayya na yi wa rikicin Boko Haram rikon sakainar kashi – Dattawan Borno

Dattawan Jihar Borno sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi wa rikicin Boko Haram da ke aukuwa a shiyyar Arewa maso Gabas rikon sakainar kashi.Sun yi zargin ne kuwa a tattaunawarsu da Aminiya inda suka ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye ta yaki hare-haren da ake kaiwa a yankin. A ranar Litinin da ta […]

Gwamnati Tarayya na yi wa rikicin Boko Haram rikon sakainar kashi – Dattawan Borno
Gwamnati Tarayya na yi wa rikicin Boko Haram rikon sakainar kashi – Dattawan Borno

Dattawan Jihar Borno sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi wa rikicin Boko Haram da ke aukuwa a shiyyar Arewa maso Gabas rikon sakainar kashi.
Sun yi zargin ne kuwa a tattaunawarsu da Aminiya inda suka ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye ta yaki hare-haren da ake kaiwa a yankin.
A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno ya gana da Shugaban kasa Goodluck Jonathan inda ya ce ’yan Boko Haram sun fi sojoji makamai da karfin hali, kuma matukar ba a kara yawan sojoji da kayan aiki ba da wuya a samu nasara a kan ’yan Boko Haram din.  
Shi ma kakakin kungiyar Dattawan Borno, Dokta Bulama Mali Gubio da yake magana kan wannan lamari ya shaida wa Aminiya a Maiduguri cewa, “Mahara na ci gaba da mummunan kisan gilla ga jama’ar Jihar Borno,” kuma Gwamnatin Tarayya tana rikon sakainar kashi ga lamarin. Gubio ya soki Shugaba Jonathan da kasa fitowa fili ya ce uffan a makonnin nan da maharan suka tsananta hare-haren da suka jawo mutuwar kusan mutum 200 a cikin mako daya.
Ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza gano ainihin matsalar da ke damun yankin ko kuma da gangan take kawar da kai a lokacin da ake halaka mutanensu da gadara.
Gubio ya ce babu dalilin da zai sa jami’an tsaro su kasa kutsawa cikin dajin Sambiza da duwatsun Mandara wuraren da mahara suke samun horo. “A lokacin Yakin Basasa sojojin Najeriya, ciki har da dubbai daga Arewa, sun hadu sun shiga rukukin dazukan yankin Gabas, inda suka shafe wata 30 suna fafatawa da ’yan tawaye har suka samu nasarar tabbatar da Najeriya a matsayin kasa daya,” inji shi.
Ya ce, “Abin kunya ne duk da yawan sojoji da kwararrun sojoji da karfin sojan Najeriya ke da shi, a ce sun kasa killace dajin Sambisa domin farautar ’yan ta’adda. Daga abin da muke gani komai kankantar kasa tana iya mamayar Najeriya kuma ta samu nasara.  Kafin a makara, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta nuna da gaske take ta hanyar samar wa sojoji da makamai tare da karfafa gwiwar sojojin, wadanda aka bar su da bindiga kirar AK 47 da albarusai kadan, yayin da a gefen ’yan ta’adda da aka ba su ingantaccen horo da karfafa musu gwiwa suke da bindigogin harbor jiragen sama da bama-bamai da gurneti da rukoki.”  
Gubio ya ci gaba da cewa, “A sauran kasashen duniya, ran dan Adam yana kima, kuma kashe mutum biyu yana iya sanya Shugaban kasa ya yi jawabin musamman ga jama’ar kasa da kuma matakan da ake dauka, ciki har da hukunta wasu mutane, amma a nan ba haka lamarin yake ba.”
Ya kara da cewa, “A fahimtarmu idan Shugaban kasar ya ki daukar matakin da ya dace domin fuskantar wannan babbar barazana, a takaice yana nuna mana mu da muka fito daga Arewa maso Gabas ba ruwansa da mu ke nan.”