Gwamnati za ta bai wa ma’aikata tallafin rage raɗaɗi a Yobe

Za a raba wa ma’aikatan Jihar Yobe Naira dubu talatin da biyar-biyar domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Gwamnati za ta bai wa ma’aikata tallafin rage raɗaɗi a Yobe

Gwamnan Jihar yobe, Maimala Buni

Gwamna Mai Mala Buni ya amince a raba wa ma’aikata N35,000 a matsayin tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa a faɗin Jihar Yobe.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin wani yunkuri da gwamnatin jihar ta yi na kawo wa ma’aikatan sauƙi sakamakon cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi tun a bara.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Jihar Yobe, Hamidu M. Alhaji ya gabatar wa Sakataren Gwamnatin jihar, Baba Malam Wali a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamna Buni ya naɗa Sakataren Gwamnatin jihar a matsayin jagoran kwamitin mai mutum shida da zai jibinci al’amuran rabon tallafin na Naira 35,000 a tsakanin ma’aikatan jihar.

Bayanai sun ce an dora wa kwamitin alhakin tantance abin da ya shafi rabon kuɗin da kuma neman shawarwarin kungiyoyin kwadago kan kuɗaɗen da za a amince da su a matsayin tallafi daga bangaren gwamnati.