Gwamnati za ta farfado da Kamfanin Citta na Kachiya

Gwamnatin Jihar Kaduna da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da kuma Bankin Duniya za su farfado da kamfanin sarrafa citta da ke Kachiya a Karamar Hukumar Kachiya da ke jihar. Jami’in Watsa Labarai na Ma’aikatar Noma da Gandun Daji na Jihar Kaduna, Malam Dahiru Abdullahi ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na […]

Gwamnati za ta farfado da Kamfanin Citta na Kachiya

Busasshiyar citta

Gwamnatin Jihar Kaduna da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da kuma Bankin Duniya za su farfado da kamfanin sarrafa citta da ke Kachiya a Karamar Hukumar Kachiya da ke jihar.

Jami’in Watsa Labarai na Ma’aikatar Noma da Gandun Daji na Jihar Kaduna, Malam Dahiru Abdullahi ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a makon jiya a garin Kaduna.

Abdullahi Dahiru ya ce, manufar Jihar Kaduna game da wannan shirin shi ne samar da sababbin wuraren sarrafawa tare da farfado da tsofaffin wuraren da aka watsar da su, inda ya ce, idan har aka tanadar da duk kayayyakin da ake bukata tare da yin aiki da su, za a samar da dimbin aiki ga matasa da kuma mata a fadin karamar hukumar.

Tuni Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya fitar da somin tabin kudi na Naira miliyan 48 a shirye-shiryen fara aikin farfado da masana’antar sarrafa citta ta Kachiya wadda aka yi watsi da ita tun shekarar 2003.

“Gwamnan Jihar Kaduna ya zagaya don duba masana’antar a cikin watan Janairu yayin da ya yi alkawarin farfado da masana’antar don rage wa manoman citta wahalar da suke sha wajen sarrafa cittar wanda hakan shi zai tabbatar da tsayayyen farashin cittar a fadin jihar.

Har ila yau, a kokarin da gwamnatin jihar ke yi don bunkasa harkar citta,  wani jami’i a  gwamnatin ya bayyana cewa gwamnatin ta shirya tsaf don samar da cibiyar adana citta mai daukar tan dubu 75, na ingantacciyar cittar da aka gyara a garin Assako da ke kusa da garin Kachiya.

“Manufar kawai ita ce a bai wa Jihar Kaduna dama a matsayinta na jihar da tafi kowace jiha noman citta a Najeriya zamowa zakaran gwajin dafin a kasa kan kayayyakinta a kasuwannin kasashen duniya.

“Cittar da ake kasuwancinta daga Najeriya ana noma ta ce a Jihar Kaduna, sannan tana daga cikin citta mafi kyau a kasuwannin duniya, sai dai abin takaici shi ne har yanzu ana bin hanyoyi na gargajiya ne wajen gyara cittar,” inji shi.