Gwamnati za ta janye takunkumin Twitter
Lai Mohammed ya ce Twitter ya amince da sharudan da Najeriya ta gindaya.
Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta daidaita tare da yiwuwar janye takunkumin da ta sanya wa dandalin sadarwa na Twitter a Najeriya.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan zaman Majalisar Zartarwa ta Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta a Abuja.
- Halin Ni-’Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan ’Yan Gudun Hijira?
- Lambar NIN ta wajaba ga masu zana jarrabawar WAEC a 2022
Lai Mohammed bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta samu daidaito da wakilan Twitter kan batutuwan suka sa ta rufe harkokin kamfanin a Najeriya.
Ya kara da cewa wakilan na Twitter sun amince da akasarin sharuddan da Gwamatin Najeriya ta gindaya musu.
A cewarsa, abin da rage a tattauna a kai shi ne batun bude ofishin Twitter a Najeriya da kuma nada babban jami’in gudanarwar da zai rika kula da ofishin a matsayin wakilin kamfanin a kasar.
Ya bayyana cewa duk da cewa Twitter ya amince da sharadin, hakan ba zai samu ba sai zuwa shekarar 2022.
Ministan ya ce nan ba da jimawa ba kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa kan tattaunawa da kamfanin zai mika rahotonsa da kuma shawarwari kan lamarin.