Gwamnati za ta jingine harajin shigo da shinkafa da alkama
Tun farkon wannan shekara Nijeriya ke fama da hauhawar farashin kayan abinci.
Gwamnatin Tarayya tana shirin dakatar da harajin shigo da kayan abinci na kwana 150 domin shigo da shinkafa, alkama da masara da sauran kayan abinci domin rage kuncin tsadar kayan abinci.
Bayanin hakan ya fito ne a kafofin sadarwar zamani gabanin taron manema labarai da Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci Sanata Abubakar Kyari zai yi.
Duk da cewa taron maneman labaran bai gudana ba, sai dai Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya ce tuni an tsara irin wannan shiri.
- Kano Pillars ta naɗa sabon mai horaswa
- Dalilai uku da ke janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da sarakuna
Ya ce an yi kuskuren yada abin ne, amma dai ana ta aiki a tsakanin Ma’aikatar Gona da sauran hukumomin da abin ya shafa, kan yadda tsarin zai samu nasarar da ake bukata.
Onanuga ya nemi afuwa kan yadda wannan kuskure ya faru, ya kara da cewa, gwamnati ta damu da halin matsin da al’ummar kasa ke ciki.
A yanzu hauhawar farashin kayan abinci ta kai kusan kashi 40.66 tun daga watan Mayu, kamar yadda Hukumar Kiddiga ta Kasa ta fitar.
Wanda hakan ya sa miliyoyin al’ummar kasar nan ba sa iya cin abinci sau uku a rana, ga kuma matsalar faduwar darajar Naira.
Aminiya ta gano cewa, bayanan da suka fito daga Ministan Noma na cewa za a aiwatar da wannan tsari har na tsawon wata biyar.
Bayanin na cewa dage harajin zai dakatar da biyan duk wani haraji a kan kayan abinci da za a shigo da shi, walau ta ruwa ko ta kan iyakokin kasa.
Sannan bayan shigowa da na ’yan kasuwa, Gwamnatin Tarayya za ta shigo da tan dubu 250 na alkama da tan dubu 250 na masara.
Takardar ta nuna cewa tun farkon wannan shekara Nijeriya ke fama da hauhawar farashin kayan abinci, inda tan daya na masara ya kai Naira dubu 850 zuwa miliyan daya.
Haka wake an ana sayar da tan daya a fiye da Naira miliyan 2, shinkafa da alkama kuma akan sayar da tan daya fiye da Naira dubu 800, ya danganta da inda aka saya.
Kayayyakin abincin da ake sa ran shigowa da su, a cewar gwamnatin za a raba su ga ƙananan kamfanonin sarrafa abinci a fadin ƙasar nan.
Bayanin ya ƙara da cewar Gwamnatin Tarayya na shirin samar da wani tsari na daidaita farashi a faɗin kasar nan, kuma za ta haɗa hannu da masu ruwa-da-tsaki wajen samar da wannan tsari.