Gwamnati za ta kara kudin tikitin jirgin kasa

A tsakiyar wannan makon ne Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara kudin tikitin shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, bayan kaddamar da karin jirage da taraga da aka aiwatar a ranar Alhamis din da ta gabata. Ministan Sufurin ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya […]

Gwamnati za ta kara kudin tikitin jirgin kasa

A tsakiyar wannan makon ne Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara kudin tikitin shiga jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, bayan kaddamar da karin jirage da taraga da aka aiwatar a ranar Alhamis din da ta gabata.

Ministan Sufurin ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa, jim kadan bayan ganawar da ministan ya yi da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce abu ne sananne cewa hatta su kan su fasinjojin sun amince da cewa ana hawan jirgin arha daga Abuja zuwa Kaduna. Ya ce shi da shugaban kasa sun tattauna batun karin jiragen da aka samu tare da tattauna cewa za a kaddamar da su a ranar Alhamis (ta jiya). 

“Shugaban kasa ya yi murna da karin jiragen, wadanda mu ke da tabbacin cewa kawo su din zai magance yawan fasinjojin da ake samu da kuma kawar da cuwa-cuwar tikiti da ma’aikatan ke yi.”

Ministan ya kuma kara da cewa za a ware jirgi daya kacokan wanda zai rika tasowa daga Kaduna zuwa Abuja kai tsaye ba tare da yada zango ko ina ba. Ya na mai cewa shi wannan jirgin zai iso Abuja ne cikin awa 1:15 zuwa 1:20, inda ya ce yana shakkar idan akwai motar da za ta iya wannan tafiyar. Sannan ya ci gaba da cewa bisa wannan mataki da gwamnati ta dauka, al’ummar Kaduna mazauna Abuja za su iya zuwa aiki a kullum cikin lokaci ba tare da sun makara ba.

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin da al’umar Najeriya ba ta gama warwarewa daga halin kuncin tsadar fetur da kuma karin kudin shiga motocin sufuri da masu motocin haya suka yi tun gabanin fara bukukuwan Kirsimeti da kuma sabuwar shekara, inda masu motocin hayar suka rubanya kudin motar hau hawa biyu zuwa uku.