Gwamnati za ta raba wa manoma taki buhu miliyan hudu

Kwamitin Takin Zamani da shugaban kasa ya kafa zai samar da takin zamani buhu miliyan hudu mai nauyin kilo 50 ga manoman kasar nan a kan farashi mai rahusa. Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan jama’a, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da […]

Gwamnati za ta raba wa manoma taki buhu miliyan hudu

Kwamitin Takin Zamani da shugaban kasa ya kafa zai samar da takin zamani buhu miliyan hudu mai nauyin kilo 50 ga manoman kasar nan a kan farashi mai rahusa.
Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan jama’a, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya  raba wa manema labarai a jiya.
Sanarwar ta nuna cewa Mataimakin Daraktan a Bangaren Yada Labarai a Fadar Shugaban Kasa, Mista Atta Esah ya ce Shehu ya yi bayanin ne a shirin Hannu Da Yawa na gidan Rediyon Kaduna day a gabata a karshen mako.
Ya ce takin wanda zai iso cikin watan Disamban mai zuwa kari ne a kan buhun taki miliyan shida mai nauyi kilo 50 da tuni aka sayarwa da manoma tun lokacin da shirin ya soma aiki a farkon shekarar nan.