Gwamnati za ta rufe kamfanin NERFUND kan bashin fiye da biliyan 17

Gwamnatin tarayya ta aiyana shirinta na rufe asusun sake gina tattalin arziki da ake kira NERFUND a takaice saboda rashin aiki da kuma kasa karbo basussukan da ya baiwa jama’a. Wata majiya da ke kusa da Ma’aikatar Kudi ta bayyana wa wakilinmu cewa tuni aka kafa kwamiti don tabbatar da rufe kamfanin a karshen watan […]

Gwamnati za ta rufe kamfanin NERFUND kan bashin fiye da biliyan 17

Gwamnatin tarayya ta aiyana shirinta na rufe asusun sake gina tattalin arziki da ake kira NERFUND a takaice saboda rashin aiki da kuma kasa karbo basussukan da ya baiwa jama’a.
Wata majiya da ke kusa da Ma’aikatar Kudi ta bayyana wa wakilinmu cewa tuni aka kafa kwamiti don tabbatar da rufe kamfanin a karshen watan Oktoba.
Majiyar ta ce ana sa ran kwamitin zai bayar da shawarwari kan alawus-alawus na ma’aikatan asusun da kuma ydda za a yi da kayayyakin ofisoshin kamfanin.