Gwamnati za ta sanya kashi 60 na manyan ayyukanta cikin kasafin kudin shekarar 2018

Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Sanata Udo Udoma ya ce gwamnatin tarayya za ta sanya kashi 60 cikin dari na manyan ayyukanta a cikin kasafin kudin shekarar 2018. Udoma ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin hadaka na majalisar dattawa kan kasafin kudi tare da Ministar Kudi, Kemi Adeosun da karamar […]

Gwamnati za ta sanya kashi 60 na manyan ayyukanta cikin kasafin kudin shekarar 2018

Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Sanata Udo Udoma ya ce gwamnatin tarayya za ta sanya kashi 60 cikin dari na manyan ayyukanta a cikin kasafin kudin shekarar 2018.
Udoma ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin hadaka na majalisar dattawa kan kasafin kudi tare da Ministar Kudi, Kemi Adeosun da karamar ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed da kuma Darakta-Janar na Ofishin kasafin kudi, Ben Akabueze.