Gwamnati za ta sayi motocin miliyan 186 ga tsofaffin shugabanni
Gwamnatin Tarayya ta ware kimanin Naira miliyan 186 don sayen motocin alfarma ga tsofaffin shugabanin kasa da mataimakansu. Wadanda za su amfana da motocin sun hada da tsaohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da Yakubu Gawon da Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abubakar Abdulsalam. Sai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar […]

Gwamnatin Tarayya ta ware kimanin Naira miliyan 186 don sayen motocin alfarma ga tsofaffin shugabanin kasa da mataimakansu.
Wadanda za su amfana da motocin sun hada da tsaohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da Yakubu Gawon da Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abubakar Abdulsalam.
Sai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo da sauransu su ma za su amfana da kudin.