Gwamnati za ta yi sulhu da masu fasa bututun mai – Babacir
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babacir Dabid Lawan ya ce Gwamnatin Tarayya tana bin hanyoyin gano tsagerun Neja-Delta domin sulhuntawa da su, Injiniya Babacir Lawan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Yola, inda ya ce, “Gwamnati ba ta yi sake ba wajen nemo ’yan asalin Niger Delta Abengers, muna son […]
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babacir Dabid Lawan ya ce Gwamnatin Tarayya tana bin hanyoyin gano tsagerun Neja-Delta domin sulhuntawa da su, Injiniya Babacir Lawan ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Yola, inda ya ce, “Gwamnati ba ta yi sake ba wajen nemo ’yan asalin Niger Delta Abengers, muna son mu san wane ne zai tsaya musu a matsayin wakilinsu domin sulhuntawa a yanzu haka. Akwai kungiyoyi da dama da suke cewa su ’yan Niger Delta Abengers ne hakan na sanya mu kasa sanin wanda ya cancanci a yi magana da shi.”
Dabid Lawal ya bukaci masu fada a ji a yankin Neja Delta su taya gwamnati wajen sulhuntawar da kuma sanya mayakan su natsu domin yaki na da illa ga kasa. “A lokacin da suka fasa bututun mai, man yana bata ruwan rafukansu, irin wannan ta’adi zai dauki shekaru da dama kafin a gyara shi kuma su za su fi kowa jin jiki,” inji shi.
Ya ce “Wannan irin ta’addanci da suke yi yana shafar man da ake fitarwa waje domin nemo kudin shiga ga kasar nan kuma yana shafar samar da wutar lantarki a kasa.”
Dangane da shirin gina yankin Arewa maso Gabas, ya ce gwamnati na da shirin da ta yi a kasa, “mun yi babbar sa’a mu mutanen Arewa maso Gabas, domin Shugaban kasa na sonmu kuma yana tausayinmu,” inji shi.
Ya cewa Gwamnatin Tarayya ta fara amfani da kudin da aka ware wajen gyara yankin da kuma sake gina shi, indab ya ce: “Za’ a kara gina Arewa maso Gabas da gyara yankin daga bana.”
Babacir ya ce akwai hukumomin da suke tallafa wa Gwamnatin Tarayya domin sake gina yankin kamar Gidauniyar Janar danjuma da Hukumar NEMA da PINE da sauransu.